--
Dahiru Bauchi ga Osinbajo: Zan nunka rokon Allah da nake maka ka gaji Buhari:-Cikakken Bayanin

Dahiru Bauchi ga Osinbajo: Zan nunka rokon Allah da nake maka ka gaji Buhari:-Cikakken Bayanin

>


 Dahiru Bauchi ga Osinbajo: Zan nunka rokon Allah da nake maka ka gaji Buhari


Bauchi - Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ranar Laraba ya ce ya jima yana rokon Allah ya ba mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, nasara a zaben shugaban ƙasa.


Jaridar Punch ta rahoto cewa Shehin Malamin ya yi alƙawarin kara nunka addu'ar da yake wa Osinbanjo.


A ranar Talata, Osinbajo, ya kai ziyara jihar Bauchi a wnai ɓangaren yawon neman shawari wurin masu ruwa da tsaki da zawarcin Deleget game burinsa a 2023.


Sheikh Bauchi ya bayyana gamsuwarsa kan Osinbajo ya ɗora daga inda shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai aje, inda ya ƙara da alƙawarin nunka rokon Allah don nasarar Osinbajo.


Malamin addinin Musuluncin ya ce:


"Zan jima ban mance wannan ziyarar ba saboda daga ƙarshe mun haɗu bayan tattaunaw aa waya. Na jima ina maka addu'a kafin yanzu da akek takara. zan nunka addu'ar da nake maka."


"Duk abinda ka sa a zuciyarka Allah zai baka, zamu goya maka baya domin nan gaba idan ka zo mana ziyara zai kasance kana matsayin shugaban ƙasar nan."


Osinbajo ya yaba wa Ɗahiru Bauchi


Tun da farko, Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya gode wa Malamin bisa kyakkyawar tarban da aka masa hannu biyu kuma ya yaba masa kan rawar da yake taka wa wajen dunƙulewar Najeriya.


Osinbajo ya ce:


"Na yi farin cikin ganin ka, saboda ka kasance ɗaya daga cikin ginshikai masu karfi na haɗin kan kasar nan da kuma hakuri game da harkokin Addini."


"Kai wani mutum ne da yake yawan magana kan zaman lafiya kuma ko da yaushe kana ƙara mana zumma. Ina sauraron karatunka a lokuta da dama wajibi na yaba maka."

0 Response to "Dahiru Bauchi ga Osinbajo: Zan nunka rokon Allah da nake maka ka gaji Buhari:-Cikakken Bayanin "

Post a Comment