--
Ba zan saki matata ba har sai ta dawo min da takardun kadarori na - Mijin Balaraba Ganduje

Ba zan saki matata ba har sai ta dawo min da takardun kadarori na - Mijin Balaraba Ganduje

>







 Ba zan saki matata ba har sai ta dawo min da takardun kadarori na - Mijin Balaraba Ganduje


Inuwa Uba, mijin Asiya-Balaraba Ganduje, diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya shaida wa wata kotun shari’a da ke zamanta a Filin Hockey, Kano cewa matarsa ​​ta shiga gidansa ta kwashe muhimman takardun kadarori, motoci da makullai da sauran dukiya.


Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa diyar gwamnan ta roki kotu da ta yi amfani da tsarin sakin aure na khul'i a addinin musulunci don raba aurenta na tsawon shekara 16 da Uba saboda ta auren ya fita a ran ta.


Don haka ta yi tayin maido masa da sadaki N50,000 da ya bayar na daurin auren nasu.


Mijin na Balaraba, wanda tun da farko ya dage cewa yana son matarsa, yanzu ya nemi ta dawo masa da takardun kadarorinsa da ababen hawa da sauran kayayyaki masu daraja da takardu kafin da ya ke zargin ta kwashe masa kafin ya amince da sakin aurenta.


Sai dai lauyan Asiya-Balaraba Ganduje, Ibrahim Nassarawa, ya musanta masaniya ga takardun da motocin da ake zargin wacce ya ke karewa ta kwashe daga gidansu a takardar shaidar da ya shigar gaban kotu.


Yayin da ya ke fatali da karar farko da lauyan Inuwa ya shigar yana kalubalantar hurumin kotun, alkalin kotun Shari’a, Khadi Abdullahi Halliru, ya dage cewa dole ne a ci gaba da sauraron karar.


Alkalin ya dage sauraron karar har zuwa ranar 19 ga watan Janairu.



SOURCE 👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Ba zan saki matata ba har sai ta dawo min da takardun kadarori na - Mijin Balaraba Ganduje"

Post a Comment