--
Kare jini biri jini akai da harin da sojoji suka kawo mana. Muba kanwar lasa bane inji KAROTA

Kare jini biri jini akai da harin da sojoji suka kawo mana. Muba kanwar lasa bane inji KAROTA

>Hukumar KAROTA ta ce an yi kare jini biri jini a farmakin da wasu sojoji suka kai ofisoshinta guda biyu a yau Juma'a.


Kwanakin baya ne dai aka samu saɓani da sojojin yayin da ƴan KAROTA ke bada hannu inda suka ƙi tsayawa, lamarin da ya haifar da rikici har da zub da jini.


Sai dai a yau jami'an sojin sun yi kukan kura inda rahotonni suka ce sun afkawa ofisoshin KAROTA sun yi musu laga-laga.


Sai dai Kakakin Hukumar Malam Nabulisi Abubakar Ƙofar Na'isa ya ce, kare jini biri jini aka yi domin jama'ar sun ɗaga wa sojojin yatsa.


Ga ƙarin bayanin da yayi mana, 

👇👇https://youtu.be/MMPMD75fF2A

SOURCE /CREDIT/Nasiru Salisu Zango via Facebook search. 


0 Response to "Kare jini biri jini akai da harin da sojoji suka kawo mana. Muba kanwar lasa bane inji KAROTA "

Post a Comment