--
Tarihin Matar Da Ta Assasa Kasuwar Sojoji (Mammy Market)

Tarihin Matar Da Ta Assasa Kasuwar Sojoji (Mammy Market)

>




Ita dai wannan kasuwa da take cikin kusan kowace Barikin Sojoji dake faɗin ƙasar nan ta soma ne tun daga shekarar 1959. Yayin da wata matashiya da ake yi wa laƙabi da Mammy Ode, daga yankin Jericho-Ugboju da yanzu yake cikin ƙaramar hukumar Otukpo dake Benue ta auri wani da ake ce mashi Anthony Aboki Ochefu, Matashin Soja wanda aka yi mashi sauyin wurin aiki zuwa jihar Enugu daga garin Abeokuta.


An


kuma basu wurin ƙwana a Barikin Sojoji dake, Abakpa, Jihar Enugu. domin Kaucewa zaman haka nan babu abin yi da kuma ƙoƙarin samun kuɗin kashewa da Ɗan abinda zata Iya taimakamawa Iyalinta, Mrs. Mammy Ochefu ta fara haɗa Kunun Zaki tana saidawa ga Sojoji, a hankali a hankali Kasuwa ta karɓu kuma tayi suna a cikin Bariki saboda Sojoji ƙanana da manya suna tururuwar zuwa Gidan ta domin sayen Kunun Zaki tsakanin Litinin zuwa Juma'a.


A kwana a tashi wata rana wani RSM yaji bai natsu da wannan sana'ar da take yi ba, inda yayi ƙorafin cewa wannan Kunun yana jawo ƙudaje zuwa cikin Bariki Dan haka ya haramta wannan sana'a.


Koda yake abun yazo mata da mamaki da kuma ban takaici cewa RSM ya umarci da adaina sarrafa kunu a Barikin, Mijinta shima yaji haushi a matsayin shi na ƙaramin Soja babu abinda zai iyayi akai domin ba zai iya bijirema hukuncin RSM ba.


Kimanin Ƴan Makwanni Mrs. Mammy Ochefu tana cikin ƙunci na rashin Kasuwancin ta, wasu manyan Jami'an Sojoji da suke jin daɗin kunun ta suka fara ƙorafi, Lamarin da ya janyo surutai a cikin Bariki Inda aka matsama RSM akan ya janye wannan Umarnin nashi.



RSM dole ya hakura ya bada Umarnin cewa a nemi wani wuri daga gefen Barikin a ba Mrs. Mammy Ochefu domin ta ci gaba da sarrafa kunun ta tana saidawa, Lamarin da yasa taji daɗi marar misaltuwa.


Daga nan fa Suma sauran Matan Sojoji ganin cewa yanzu an ware wuri na musamman domin Kasuwanci Suma sai suka fara cin Albarkacin ta tare da kawo nasu sana'oin suna saidawa, wannan shine asalin yadda sunan "Mammy Market" ya samu.


Bada jimawa ba da aka bada wannan wurin kuma sai ga doka tazo daga sama cewa a ware wani wuri a kowace Barikin dake faɗin ƙasar nan domin gina irin wannan kasuwar, daga nan ne itama ta samu damar Gina ƙaramin shago, daga nan Kasuwancin ta ya habbaka.


Bayan juyin mulkin da aka hambarar da Janar Yakubu Gowon, Anthony Aboki Ochefu, a lokacin ya zama Colonel, an tura shi yankin Kudu a matsayin Gwamnan Mulkin Soji, wannan dalilin yayi sanadiyyar komawar Mrs. Mammy Ochefu da Mijinta zuwa Enugu a matsayin First Family; 


Wani Lokacin takan je ziyara kasuwar Mammy Market da ta fara kimanin Shekaru Goma Sha Shidda a lokacin, bayan da kuma Mijin nata, Colonel Anthony Aboki Ochefu yayi ritaya daga aikin Soji sai suka kafa wani Kampanin dakon kaya da suka raɗa mashi suna, Mammy Markets, har yanzu dai Mrs. Mammy Ochefu tana nan a raye a garin Otukpo na jihar Benue.

SOURCE : Rariya on Facebook. 


0 Response to "Tarihin Matar Da Ta Assasa Kasuwar Sojoji (Mammy Market)"

Post a Comment