ICPC na bincikar jakadan Nijeriya a Morocco bisa wawure dala dubu 200.

 

ICPC na bincikar jakadan Nijeriya a Morocco bisa wawure dala dubu 200 don gyaran gidansa


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta gayyaci jakadan Najeriya a Morocco, Al-Bashir Ibrahim Saleh, bisa zarginsa da kashe dala dubu 200 don gyara gidansa na zama da ke Souissi a birnin Rabat na kasar Morocco.


Wasu majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa ana sa ran jami’in diflomasiyyar zai gurfana a gaban hukumar a yau Talata.


A cewar majiyoyin, jakadan yana tafiyar da harkokin ofishin jakadancin ba tare da bin ka’ida ba.


Wasu majiyoyi a gidan Tafawa Balewa, ma’aikatar harkokin wajen Naieriya, sun ce ma’aikatar ta kuma samu korafe-korafe kan zargin wawashe asusun ma'aikatar da wasu munanan dabi’u da ke rage kima da martabar ofishinsa.


A wata wasika da hukumar ta ICPC ta aikewa ma'aikatar harkokin wajen kasar, ta umurci ma'aikatar da ta kira jakadan domin amsa tambayoyi.


“Hukumar na bincike kan zargin karya dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka ta shekarar 2000 da kuma bin sashe na 28 na dokar, ana bukatar ma’aikatar ta dawo da Ambasada Al-Bashir IS. Al-Hussaini (Shugaban Ofishin Jakadancin na Najeriya Rabat, Moroko zai bayyana a gaban wadanda aka sanya wa hannu a sashin bincike, hedkwatar ICPC Abuja a ranar Talata 15 ga Nuwamba, 2022 da karfe 10 na safe,” in ji wani ɓangare na wasikar.


SOURCE : DAILY NIGERIAN HAUSA ON FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments