--
Kano state, zamu tabbatar da wayar da kan dalibai akan illar shaye shaye

Kano state, zamu tabbatar da wayar da kan dalibai akan illar shaye shaye

>

 
Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin wucin gadi da zai wayar da kan daliban manyan makarantun gaba da sakandire kan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran matsalolin tabin hankali.


Mataimaki na musamman kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Fauziyya Buba, ta bayyana hakan a wajen taron wayar da kan jama’a na kwana daya a ranar Juma’a.


Buba, wacce itace shugaban kwamitin kula da lafiyar kwakwalwa na jihar kuma kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na mata, ta ce an kira taron ne domin duba shawarwarin da aka bayar a taron da ya gabata.


Ta bayyana cewa, a taron farko da akayi, an ba su matakan aiki bisa ayyukan da aka bayyana, wanda ya kai ga kafa sashin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a sassan manyan makarantun jihar. .


Source 👉Rahama Tv on Facebook. 

0 Response to "Kano state, zamu tabbatar da wayar da kan dalibai akan illar shaye shaye "

Post a Comment