--
 An Zargi Jami'an Tsaro Da Kama Matashi Al'Amin Bayan Ya soki  Aisha Buhari a twitter

An Zargi Jami'an Tsaro Da Kama Matashi Al'Amin Bayan Ya soki Aisha Buhari a twitter

>

 
An Zargi Jami'an Tsaro Da Kama Matashi Al'Amin Bayan Ya Ci Zarafin Aisha Buhari


Baki shi ke yanka wuya, in kasan mai zaka fada baka san mai zaije ya dawo ba, sannan magana zarar Bunu ce in aka furtata sai abun muka gani.


Wani matashi a twitter mai suna Aminullahie ya yi amfani da hotan uwar gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammad Buhari yayi mata rashin kunyaa inda ya rubuta "Su Mama Anchi Kudin Talakawa An Koshi" inda a yanzu ake zargin jami'an tsaro villa da kama shi, kuma anje har jamiar da yake karatu ne aka kama shi a garin Dutse dake Jigawa. 


Da fari zan so 'yan Nijeriya su sani cewa tabbas dan mun kasance muna da waya da data ba shi zai ba mu dama mu ci mutucin manyan mu ba, musamman iyaye mata, hajiya aisha Buhari mahaifiya ce kamar kowa, tana yara da jikoki, kiran ta da taci kudin talakawa tamkar kiranta da tayi sata ne wanda babu wani makusancin, duk wani nata in yagani bazai ji dadi ba, duk wani masoyin ya bazai Ji dadi ba, yadda in aka zagi mahaifiyar mu bazamu ji dadi ba haka ita ma.


Yanzu an ce an bi wannan yaron har jami'ar dutse an kama sho wanda ba a da tabbacin suwa suka kama shi, sai dai a twitter ana zargin cewa kama shi yana da alaka da wannan rubutun, sannan jami'an tsaro ne daga Villa Suka Kama Shi, wannan ma zargi ne tun da ba a da tabbas.


Ya kamata ace mu san mai zamu na rubutawa akan mutane, in ma kana da problem da mutum ba dole sai ka ambaci sunan shi ko sai ka sanya hotan shi sannan ka kira shi da muggan kalmomi.


Ya kamata ace mun kiyaye mun shiga taitaitayin mu, Allah swt ya kiyaye gaba, in ta tabbata maman mu ne ta ke bin hakkin ta, muna rokkon ta da tayi hakuri ta yafe ma wannan matashin.


Allah ya kiyaye gaba.


Daga Usman Rabiu Kwankwaso

CREDIT /SOURCE 👉Rariya /Facebook 


0 Response to " An Zargi Jami'an Tsaro Da Kama Matashi Al'Amin Bayan Ya soki Aisha Buhari a twitter "

Post a Comment