--
Yarima bin Salman zai baiwa yan kwallon saudiyya motar kirar Rolls Royce Phantom

Yarima bin Salman zai baiwa yan kwallon saudiyya motar kirar Rolls Royce Phantom

>

 
Yerima mai jiran gado a Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya yi alkawarin bai wa kowanne daga cikin ‘yan kwallon kasar da suka suka yi nasara a kan 'yan wasan Argentina, kyautar motar alfarma kirar Rolls Royce Phantom.


Yeriman na Saudiyya, ya nuna farin ciki ne da nasarar da kasar ta samu musamman ganin cewa Lionel Messi da kansa na cikin wasan da suka fafata a ranar Talata. 


Kimanin dalar Amirka dubu 460 ne dai kudin kowace motar ta Rolls Royce Phantom yake.


Me kuka ce?


Source /credit DW Hausa / Facebook. 

0 Response to "Yarima bin Salman zai baiwa yan kwallon saudiyya motar kirar Rolls Royce Phantom "

Post a Comment