--
DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100

DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100

>Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bawa matasa 152 tallafin Naira N100m. Matasan da suka yi watsi da harkar daba a wata Ƙungiya.

Wannan na zuwa ne biyo bayan kammala shirya musu na tsawon wata guda na horo na tsanaki kan harkokin kasuwanci.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wasu matasa 152 da suka yi gyare-gyare wadanda suka kasance fitattun ‘ya’yan wata kungiyar ‘yan daba ta siyasa mai suna ‘ECOMOG’ a Maiduguri.

Zulum ya basu wannan kudi ne domin su ja jari, su samu kasuwanci da zasu rika ciyar da iyalansu, Don samu ingantacciyar rayuwa

0 Response to "DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100"

Post a Comment