DA DUMINSA: Sojojin Najeriya sun Hallaka kwamandan ‘yan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno
Friday 18 February 2022
Comment
Rahotannin da ke shigo mana sun nuna cewa jami’an tsaron Sojojin Najeriya, sun yi nasarar kashe miyagun ‘yan ƙungiyar ISWAP da dama sun Kuma kashe babban kwamandansu a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 13 ga watan Fabrariru na Shekarar 2022, a wani harin kwantan bauna da suka Kai masu.
An samu tabbacin cewa sojojin Najeriya sun kai farmakin a jirgin A-29 Super Tucano a ranar 13 ga Fabrairu, 2022, sun kashe babban kwamandan ISWAP, Malam Buba Danfulani da wasu mayaka da dama a gefen tafkin Chadi a karamar hukumar Kukawa da ke jihar Borno.
0 Response to "DA DUMINSA: Sojojin Najeriya sun Hallaka kwamandan ‘yan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno"
Post a Comment