--
Zukekiyar Baturiya ta Dira a Najeriya Domin Masoyinta duba cikakken bayanin yadda suka hadu>>>

Zukekiyar Baturiya ta Dira a Najeriya Domin Masoyinta duba cikakken bayanin yadda suka hadu>>>

>


Wasu masoya biyu sun nunawa duniya cewa soyayya ta wuce karfin launin fata ko kasa kuma so makaho ne Baturiyar matar ta bar kasarta inda ta dira Najeriya saboda ta samu ganin masoyinta dan Najeriya A wani bidiyon masoyan, 


an gansu suna shagali tare da soyewa tare, lamarin da ya janyo maganganu a kafar sada zumunta Wasu masoya biyu sun jijjiga kafafen sada zumunta da salon soyayyarsu. 


Abinda ya fi baiwa jama'a mamaki kuma yasa suka dinga magana shine ganin banbancin launin fatarsu. @gossipboyz1 ta wallafa bidiyon a Instagram kuma tana bada labarin yadda baturiyar ta garzayo har Najeriya domin haduwa da masoyinta. 


Shafin ya wallafa: "Soyayya ruwan zuma, bata san nisa ba. Ta garzayo daga Turai har Najeriya domin haduwa da masoyinta." 


'Yan Najeriya sun yi martani: 

 @_blingsexchange martani tayi da: "Abu kadan da muke jira mu yi wuff... Ba haka ake yi ba fa." 


@yemishark rubutawa tayi: "Soyayya tana da dadi irin haka. Baba zai tsere..." 


@king_vicky_tyann tsokaci yayi da: "A ina kuke nemo irin wannan soyayyar, ina zan samu so na gaskiya.?" 


@xtian_crystal mamaki tayi tare da cewa: "A ina kuke ganin irin wannan soyayyar?" 


Source: Legit

0 Response to "Zukekiyar Baturiya ta Dira a Najeriya Domin Masoyinta duba cikakken bayanin yadda suka hadu>>>"

Post a Comment