--
Kalli Hoto: Yadda Ƙaburbura 650 suka rufta sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye makabarta

Kalli Hoto: Yadda Ƙaburbura 650 suka rufta sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye makabarta

>


Ambaliyar ruwar zama da ya faru bayan ruwan sama ya janyo kaburbura sun rufta a garin Gashua da ke jihar Yobe 


Wasu mazauna garin sun ce a kalla kaburbura 650 ne suka rufta sakamakon ambaliyar da ya mamaye wurare da dama a garin Mazauna garin sun yi kokarin bude hanyoyin ruwa domin saukaka lamarin amma duk da haka sun nemi a kai musu dauki 


A kalla kaburbura 650 ne suka rufta a babban makabartar garin Gashua da ke karamar hukumar Bade a jihar Yobe sakamakon ambaliyar ruwa da ya mamaye wasu yankunan garin. 


Daily Trust ta ruwaito cewa ambaliyar ruwan ya mamaye makabartar ne bayan ruwan sama da aka yi a ranar Asabar. 


Abinda mutanen gari suka ce game da ambaliyar ruwan 


Daily Trust ta ruwaito cewa wani shaidan gani da ido, Idris Anthony Brah, wanda ya ziyarci makabartar ya nuna damuwa matuka game da abin da ya faru. 


Ya ce: "Kaburbura da dama sun rufta kuma ana iya ganin wasu gawarwakin da aka birne, wanda hakan ya tilastawa mazauna garin yin tururuwa zuwa makabartar. 


"Mun dauki kayayyakin aikin mu mun haka hanyoyin ruwa saboda mu rage ruwan da ya taru a makabartar kada ya lalata sauran kaburburan." 


Wani mazaunin garin mai suna Yahaya Mato, ya ce lamarin ya fi karfinsu don haka sun dai iya abin da za su iya wurin rage ruwan da ke kwance a makabartar. 


Mato ya ce wasu sassan katangar da aka zagaye makabartar ya rushe. Ya yi kira ga gwamnati da mutane masu hali su taimaka domin a gyara kaburburan. 

0 Response to "Kalli Hoto: Yadda Ƙaburbura 650 suka rufta sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye makabarta "

Post a Comment