--
Zamu maka duk wani malami daya qara sukar Sheikh Abduljabbar A Kotu - Inji Lauyoyinsa,  Saurari Sautin Murya>>>

Zamu maka duk wani malami daya qara sukar Sheikh Abduljabbar A Kotu - Inji Lauyoyinsa, Saurari Sautin Murya>>>

>Shehin malamin ya bayyana dakatarwar da gwamanatin Jihar Kano ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".


Shiekh Abduljabbar ya faɗa wa BBC cewa duk da ita gwamnati da kanta, ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar, ta tabbatar da abin da ake yi masa zalunci ne, amma ta dakatar da shi ba tare da ba shi damar kare kansa ba.


Abduljabbar dai na waannan kalami ne biyo bayan rufe makarantarsa da masallacinsa da gwamantin Kano ta sanar da yi a ranar Laraba tare da haramta saka karatunsa a kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai a jihar.


Shehin malamin ya ce taron da ya gudanar a makon da ya gabata na daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin, ganin cewar duk yunƙurin hana taron ya ci tura.


Gwamnatin Jihar kano tasha Alwashin hada malaman jihar kano da sheikh Abduljabar guri guda domin gudanar da muqabala a tsakaninsu wanda har yanzu ba'a san inda aka kwanaba,  game da muqabalar ba, 


Kwatsam daga baya anjiyo wani faifan bidiyo mai dauke da sautin muryar lauyan Kungiyar Ashabul Khafi,  Inda Yake Bayyana Cewa Sun Dauki matsakin Shari'a Da Duk Wani Mutum Ko Malami ne wanda ya qara Yada Cewa Shehin Malamin Yaci zarafin Annbi (S), 


Gadai sautin muryar kauyan nasa nan cikin bidiyo a qasa Latsa Nan👇

 


0 Response to "Zamu maka duk wani malami daya qara sukar Sheikh Abduljabbar A Kotu - Inji Lauyoyinsa, Saurari Sautin Murya>>>"

Post a Comment