--
Yanzu-Yanzu: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi

Yanzu-Yanzu: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi

>


Yan Boko Haram sun kai hari yanki a jihar Yobe da safiyar Alhamis a cikin motar sulƙe Maharan sun mamaye ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na safe, 


yayin da mutanen garin suka arce Wasu mazauna ƙauyen sunce da yuwuwar yan ta'addan sun zo ɗibar kayan abinci ne 


Wasu da ake zargin yan ta'addan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Katarko mai nisan kilomita 18 tsakaninsa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kamar yadda channels tv ta ruwaito. 


Mazauna garin sun shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 10:00 na safe a cikin motar sulke ta yaƙi da kuma motoci Hilux guda 6 ɗauke da bindigun kakkaɓo jirgi. 


Wasu mazauna ƙauyen da suka tsere cikin daji domin tseratar da rayuwarsu, sun bayyana cewa suna tsammanin yan ta'addan sun zo satar kayan abinci ne saboda yau Alhamisa ranar Ƙasuwar ƙauyen Katarko ce. 


"Muna ganin sun zo ɗibar kayan abinci ne saboda ranar Alhamis itace ranar da kasuwa take ci a ƙauyen Katarko," inji su. 


Sojoji sun musu kwantan ɓauna Wata majiya ta bayyana cewa jami'an soji sun yi wa yan ta'addan kwantan ɓauna yayin da suke ƙoƙarin komawa sansanin su. 


Harin ƙarshe da aka kai Ƙauyen Katarko shine wanda aka kai ranar 16 ga watan Maris, inda yan ta'addan suka lalata gine-gine wurin kula da lafiƴar mutane. Cikakken bayani zai biyo baya 


Source: Legit.ng 

0 Response to "Yanzu-Yanzu: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Jihar Yobe da Motocin Yaƙi "

Post a Comment