--
Da duminsa: Gwamnatin kano ta tabbatar da ranar da za'ayi Mukabala Da Abduljabbar Duba cikakken bayani>>>

Da duminsa: Gwamnatin kano ta tabbatar da ranar da za'ayi Mukabala Da Abduljabbar Duba cikakken bayani>>>

>


Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanya ranar da za a tafka mukabala tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman jihar.


Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahar Adamu wanda ake kira Baba Impossible ne ya bayyana haka ranar Alhamis a tattaunawarsa da BBC Hausa.


Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan nan na Yuli a birnin na Kano.


A cewarsa tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga malamin da malaman da za su fafata da shi.


Kwamishinan ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan shugabannin zauren hadin kan malaman Kano sun zargi gwammatin jihar da "jan kafa" game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa. Ya sha musanta wannan zargi.


A ranar Laraba ne wata Babbar kotun Kano ta amince da bukatar lauyoyin Sheikh Abduljabbar kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin.


Alkalin kotun, Mai shari'a Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la'akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.


Da ma dai Sheikh AbdulJabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".


Ranar 4 ga watan Fabrairun da ya wuce ne majalisar zartarwar jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar, saboda furta kalaman tunzuri a yayin wa'azi da kuma kalaman batanci ga Annabi Muhammad.


A wancan lokacin gwamnatin ta shaida wa BBC cewa ta yi nazari kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, ciki har daga manyan malamai da hukumomin tsaro, kan kalaman da malamin ke furtawa, shi ya sa ta dauki wannan mataki.


Tun a wancan lokaci ne gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike a kan wadannan zarge-zarge, amma har yanzu bai gabatar da rahotonsa ba.


Shi dai Malamin ya yi zargin cewa gwamnatin Kano ba ta yi masa adalci ba wajen daukar matakin ba tare da an ji daga nasa bangaren ba.


Ya nemi a shirya masa zama da malaman dake ƙalubalantarsa domin ya kare duk abin da yake faɗi, bukatar da gwamnatin ta amince da ita, kafin daga bisani kotu ta haramta yin zaman kasa da awanni 48 kafin a gudanar da shi.


Source: Bbc Hausa

0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin kano ta tabbatar da ranar da za'ayi Mukabala Da Abduljabbar Duba cikakken bayani>>>"

Post a Comment