--
Da duminsa: Gwamnatin jihar Kano ta rushe hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli (REMASAB) Duba dalili>>>

Da duminsa: Gwamnatin jihar Kano ta rushe hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli (REMASAB) Duba dalili>>>

>



Daga: Fatima Abdullahi Hotoro

Gwamnatin jihar Kano ta rushe hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli ta jihar Kano wato REMASAB.


Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da ‘yan jaridu.


Ya ce gwamnatin Kano ta rushe hukumar, sai dai babu wani ma’aikaci ɗaya da zai rasa aikin sa, domin kuwa an yi tsarin rarraba ma’aikatan hukumar zuwa wasu hukumomin, su kuwa ma’aikatan wucin gadi an mikawa wani kamfanin Wanda suka sanya Hannu kan yarjejeniya da shi.


Ya ce, tuni gwamnati ta dauki matakin sauya salon sarrafa shara ta hanyar hadin guiwa da wani kamfani mai zaman kan sa da zai rika sarrafa shara, don ta zamo takin zamani da iskar gas da kuma wutar lantarki.


Kwamishinan ya ce kamfanin zai rika biyan gwamnati naira miliyan 50 a shekarar farko-farkon yarjejeniyar, a shekarun gaba Kuma ya rika biyan miliyan 100, haka zalika a shekarun karshen karshe na yarjejeniyar kamfanin zai rika biya naira miliyan 200 a duk wata.


kwamishinan muhalli

Getso ya kuma ce, kamfanin zai ɗauki ma’aikata sama da dubu hudu ciki har da injiniyoyi, kuma za su ninka albashin ma’aikatan da aka basu har sau uku.

0 Response to "Da duminsa: Gwamnatin jihar Kano ta rushe hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli (REMASAB) Duba dalili>>>"

Post a Comment