--
Kalli Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Kalli Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

>


Hukumar yan farin kaya DSS ta fara neman dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo 


Yan sandan sirin na Nigeria, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli sun tabbatr da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo 


DSS, yayin taron manema labarai da ta kira ta yi holen a kalla mutane 12 da ta kama tare da bindigu, makamai da layu da guraye da wasu kayan da ta kama a gidansa


Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo. 


Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo. 


An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 


Peter Afunanya, mai magana da yawun hukumar DSS yayin taron manema labaran a Abuja ya yi holen a kalla mutum 12 (11 maza, mace1) da aka kama yayin samamen.


Kayayyakin da DSS ta gano a gidan Sunday Igboho Wasu daga cikin kayayyakin da aka gano a gidan dan gwagwarmayar na Yarbawa sun hada da guraye, layu, makamai, wayoyin salula, fasfo da sauransu. 






Hukumar ta ce a halin yanzu Igboho ya tsere amma Afunanya ya shawarce shi ya mika kansa domin babu shakka gwamnati za ta gano shi. 


0 Response to "Kalli Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo "

Post a Comment