--
Dakta Nasíru Yusuf Gawuna Shi Né Ya Fi Cancanta Ya Zama Gwamnań Kanó A Zaɓén 2023 - Shaíkh Badaru Sallau

Dakta Nasíru Yusuf Gawuna Shi Né Ya Fi Cancanta Ya Zama Gwamnań Kanó A Zaɓén 2023 - Shaíkh Badaru Sallau

>

Dakta Nasíru Yusuf Gawuna Shi Né Ya Fi Cancanta Ya Zama Gwamnań Kanó A Zaɓén 2023 - Shaíkh Badaru Sallau 


Shaíkh Badaru Sallau Hassan, mai nazari da fashin baƙi kan al'amuran yau da kullum ya shawarci al'ummar Jihar Kano da su zaɓi ɗan takarar jam'iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamnan Jihar Kano 2023.


Sheíkh Sallau wanda ya bayyana haka a wannan rana, ya nuna cewa duk wata nagarta da cikar kamala da ake buƙata ga shugaba Dakta Gawuna ya na da su dan haka babu wani mutum da ya dace ya zama gwamnan Jihar Kano a yau sama da shi.


"Ina shawartar mutanen Jihar Kanó su yi duba da yadda zaɓen shugaban ƙasa ya gudana. Mutane sun fito sun zaɓi cancanta batare da an ba su ko kwabo ba domin nagarta ake nema. 


Dan haka ni ɗan Jihar Kano ne kuma zan fito ranar zaɓe na zaɓi Gawuna tare da iyalina da duk wanda na isa da shi saboda shi ne ya fi cancanta ya zama gwamnanmu a wannan shekara, kuma ina shawartarku ku zaɓe shi".


Mallam Badaru ya kuma ƙara da cewa: "Dakta Nasiru Gawuna dattijo ne, mutum ne mai magana ɗaya, ba shi da abokan faɗa a Jihar Kano da wajenta. 


Mutum ne mai girmama manya da mutunta na ƙasa da shi, ba shi da girman kai da raina mutane kowa nasa ne. Mutumin da ya ke da waɗannan kwaliti shi ne ya fi dacewa da ya shugabanci al'umma". -Shaíkh Badaru.


CREDIT/ Dokin karfe TV via Facebook search. 

0 Response to "Dakta Nasíru Yusuf Gawuna Shi Né Ya Fi Cancanta Ya Zama Gwamnań Kanó A Zaɓén 2023 - Shaíkh Badaru Sallau "

Post a Comment