--
ZAƁÈN 2023: Kungiyar ANA Ta Taya Tìnúbú Murna, Ta Gargadi Obasanjo Kan Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasâ

ZAƁÈN 2023: Kungiyar ANA Ta Taya Tìnúbú Murna, Ta Gargadi Obasanjo Kan Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasâ

>







 ZAƁÈN 2023: Kungiyar ANA Ta Taya Tìnúbú Murna, Ta Gargadi Obasanjo Kan Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasâ 


Kungiyar Arewa New Agenda, ANA, a ranar Laraba, ta gargadi tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, kada ya tada rikici a kasar da maganganu da kiraye-kiraye da ya ke yi na a soke zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu. 


ANA, wacce kungiya ce ta hadin kan Arewa, karkashin jagoranta, Sanata Ahmad Abubakar Moallahydi, yayin taron manema labarai da aka yi don kwantar da hankula bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da INEC ta yi, ya yi kira ga yan Najeriya su bawa zababben shugaban kasar goyon baya sannan su yi watsi da kiran tada rikici. 


Moallahydi ya ce babu bukatar taron manema labarai da Obasanjo ya kira kuma a yi watsi da shi, rahoton Vanguard. 


Ya kuma ce INEC ta yi zabe na adalci inda ya bada misali da jihohin Legas, Kano, Plateau, Nasarawa, Gombe, Katsina, Ebonyi, Anambra, Delta, Kaduna da Yobe inda jam'iyyun hamayya suka yi nasara. 


Ya ce: "ANA, a madadin dimbin mutanen arewa wanda suka fito suka zabi mai girma Sanata Bola Ahmed Tinubu, muna taya Asiwaju Ahmed Bola Tinubu zababben shugaban tarayyar Najeriya murna. 


"Wannan nasara ce ga Najeriya. Bisa la'akari da hadin kan kasa, muna fatan ganin sabuwar Najeriya kuma muna kira ga sauran yan kasa su taho su hada kai mu tallafawa gwamnati mai shigowa don ta daukaka kasar." 


Martanin ANA Ga Obasanjo


"Hakazalika, muna gagawan mayar da martani wasu mutane masu wata bukatan kansu wadanda maganganunsu ya ci karo da tsarin zaman lafiya musamman tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. 


"Mun karanta sanarwar da Obasanjo ya fitar na kira ga shugaban INEC ya yi biyayya ga wasu ra'ayoyin (Obasanjo) wadanda kamar yadda ake tsammani ya bazu a gari kamar yadda muka yi imani nufinsa kenan; a ciki ya bayyana ra'ayinsa kan yadda ya ke son a yi zaben kasa na 2023. "Mun tabbatar ya san cewa kalamansa ya janyo mahawara da martani daban-daban a kasa; mutane sun kalli abin da fuskoki daban-daban bisa ra'ayinsu na siyasa da na kashin kansu. 


"Abin da ya fi muhimmanci shine mutumin da ya tada maganan; bari in fayyace wani abu: ya yi shugaban kasa sau biyu a karkashin dimokradiyya (1999-2007); kuma janar ne mai ritaya (wanda ya yi kasa yaki) kuma dattijon kasa. Ya cancani hakan kuma muna girmama shi." 


Ya cigaba da cewa: "Amma, mun nesanta kan mu daga sha'awarsa na rura wutar yanki, kabilanci da bangaranci. 


"Muna tuna masa yunkurin da ya yi na murkushe dimokradiya, kamar neman zarcewa karo na uku wanda yan Najeriya suka tsinkaya, har yau abin kyama ne. 


"Matsayarsa a sanarwar ya kara zurfafa fahimtar munafinci da ke tattare da irin siyasarsa; ya manta cikin sauki cewa ya fada wa kasa ya dena siyasar bangaranci - kada a ji gangunan yaki daga bayan gidansa." 


"Gargadin mu gare shi shine ya fahimci iyakar siyasarsa ta kasuwanci. Babu matsala lokacin da ya amfana daga arewa amma yanzu da lokacin wani ne, yana fushi da takaici saboda ba batunsa ake ba. Hakan bai maka kyau ba, ba zai yiwu kullum kai ne ba."


ANA ta yi kira ga yan Najeriya su nesanta kansu daga sakon Obasanjo ANA ta yi kira ga al'ummar Najeriya na gari su nesanta kansu daga sanarwar manema labarai da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fitar domin yana kokarin raunana mana dimokradiyya ce da mutanen mu suka yi wa hidima tun bayan da INEC ta fitar da dokokin zaben 2023, tana mai kira ga duk wanda ke da korafi ya bi tsarin da doka ta tanada. 


Daga karshe, kungiyar ta yi kira ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi jawabi ga yan Najeriya don kwantar da hankulansu kamar yadda ya yi alkawari. 


Kungiyar ta kuma karfafawa shugaban INEC gwiwa ya zama mai juriya wurin yin babban aikin da ya ke wa kasa.


CREDIT /Dokin karfe TV via Facebook search. 

0 Response to "ZAƁÈN 2023: Kungiyar ANA Ta Taya Tìnúbú Murna, Ta Gargadi Obasanjo Kan Yi Wa Dimokradiyya Zagon Kasâ "

Post a Comment