--
Kotu ta umarci a kamo Abdullahi Abbas bisa zargin barazanar ga rayuwa da tada hankali

Kotu ta umarci a kamo Abdullahi Abbas bisa zargin barazanar ga rayuwa da tada hankali

>






Kotu ta umarci a kamo Abdullahi Abbas bisa zargin barazanar ga rayuwa da tada hankali


Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin a gaggauta kama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya, bisa zargin laifin barazana ga rayuwa, tada hankali da kuma kalaman ɓatanci.


Mahmoud Lamido, ɗan gwagwarmaya a jihar Kano kuma shi ne abin ya shafa, ya garzaya kotu ta hannun lauyansa, Bashir Tudunwazirirchi, ya na neman a gaggauta kama shugaban jam’iyyar ta APC Abdullahi Abbas, bisa zarginsa da yi masa barazana ta wayar tarho, ta hanyar cewa "sai na batar da kai".


Mai shari’a, S.A. Amobeda na babbar kotun tarayya mai zamanta a Kano ya bayar da wannan umarni tare da ɗage zaman zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu domin sa ido kan ko za a bi umarnin.


Da ya ke mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa, kakakin jam'iyyar adawa ta NNPP, Sanusi Dawakin Tofa ya ce wannan ne karo na biyu a jere da alkalai daban-daban suka bayar da irin wannan umarnin kotu, domin tilasta wa kwamishinan 'yan sandan kamawa tare da gurfanar da Abbas a gaban kuliya kan batutuwan da suka shafi tashin hankali, tsoratarwa da barazana ga rayuwa.


"Muna fatan wannan zai zama darasi ga duk wani dan siyasa da ya zabi hanyar tashin hankali, maimakon inganta zaman lafiya a Kano da Nijeriya," in ji Mista Dawakin Tofa.


Source, Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 


0 Response to "Kotu ta umarci a kamo Abdullahi Abbas bisa zargin barazanar ga rayuwa da tada hankali"

Post a Comment