--
WANI ABU SAI YA'YA MATA πŸ’ͺ

WANI ABU SAI YA'YA MATA πŸ’ͺ

>WANI ABU SAI YA'YA MATA πŸ’ͺ


_ Mace zata iya yin Blocking Dinka, takuma goge Lambarka sannan tace kada Ka kara kiranta har Abada. Amma sai ta koma gefe tana jiran ganin sakonka. Kada ka tambayeni Dalili, domin matane kadai zasu iya yi maka Bayani.


_ Ɗan uwa inaso ka Sani ita fa Macen da take mutukar kaunarka da Gaskiya zata iya yin "Blocking" Dinka a WhatsApp, Facebook, sannan ta dinga karbar wayar kawayenta tana dubawa taga yadda kake tafiyar da Al'amuranka ko Don taji sanyi cikin ranta.


_ Zasu iya furta maka munanan kalamai da nuna cewa alaka ta Kare a tsakaninku a gabanka. Amma a gefe guda zata kwaranyar da Hawaye Mai radadi a saboda kaunarka. Zuciyar Mata na da Mutukar taushi fiye da tafukan kafar Jariri.


_ Macen dake mutukar kaunarka, zata iya yin fada da kai, Kuma ta kwanta Gado daya tare da kai, sannan ta bada tazara a tsakaninku Wanda Mutum 10 za su iya shiga tsakaninku. sannan a hankali ta dinga juyowa domin ta gani ko ita kake kallo ko Kuma ka juya Mata Baya, duk a saboda kaunarka.


_ Abinda nakeso nace shine, Kada ka Ι—auki Mataki akan wasu kalamai da Mace ta Furta maka a Lokacin da take cikin fushi, domin mafi yawan Lokutan da suke cikin fushi abinda suka furta ba shineh har cikin Zuciyarsu ba.


Allah ya muku Albarka yaku nisa'u ya wadatamu da abinda zamu baku ya kuma bamu ikon Hidinta muku ko da last card din mu ne.


SOURCE, SIRRIN RIKE MIJI ON FACEBOOK SEARCH. 

0 Response to "WANI ABU SAI YA'YA MATA πŸ’ͺ"

Post a Comment