--
India za ta bai wa ƴan Nijeriya guraben tallafin karatu 500 -- Wakili

India za ta bai wa ƴan Nijeriya guraben tallafin karatu 500 -- Wakili

>

 






India za ta bai wa ƴan Nijeriya guraben tallafin karatu 500 -- Wakili


Shri Balasubramanian, Babban Wakilin India a Nijeriya, ya ce kasar za ta bayar da guraben tallafin karatu 500 ga ƴan Nijeriya a shekarar 2023.


Balasubramanian ya bayyana haka ne a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Abuja.


Wakilin ya ce ziyarar aikin da ya kai hukumar ita ce don inganta bayanai da musanyar sadarwa tsakanin kasashen biyu.


Balasubramanian ya ce, "Za mu gayyaci ƴan jarida daga Nijeriya su tafi Indiya, ba wai su yi karatu ba, " a zahiri ziyarar da ake shirya wa don bayyana Indiya ce.


“Wato abin da Indiya ke yi a fagen siyasa. Ba za mu yi shi ne kawai ga Nijeriya ba, amma ga Afirka ta Yamma, kusan mutane 30.


“Na tabbata Nijeriya, kasancewarta a cikin kungiyar G20, za ta iya samun karin adadi, don haka za mu yi hakan bayan watannin Maris da Afrilu.


“Zan tattauna da ku don samun shawarwarinku kuma; muna bayar da tallafin karatu 500 kowace shekara ga ƴan Najeriya, 250 daga cikinsu na bangaren farar hula.


"Za mu yi farin cikin sake gabatar da karo karatu a fannin ilimin jarida a wani wuri mai daraja kuma muna da kwasa-kwasai na gajeren zango ."

SOURCE, DAILY NIGERIAN HAUSA VIA FACEBOOK SEARCH. 

0 Response to "India za ta bai wa ƴan Nijeriya guraben tallafin karatu 500 -- Wakili"

Post a Comment