--
Ba zancen gadon Masallaci, so muke ayi tsari mai inganci don Dore war iyalan DR Ahmed buk.

Ba zancen gadon Masallaci, so muke ayi tsari mai inganci don Dore war iyalan DR Ahmed buk.

>
Iyalan Babban Malami marigayi Dr. Ahmad Ibrahim BUK sun musanta iƙrarin da Dr. Umar Indabawa ya yi a kansu.


Dr. Indabawa ya zargi ƴaƴan marigayi Dr. Ahmad da hana ruwa gudu wajen ci gaban Masallacin Darul Hadith har ma ya ce a cikinsu babu wanda zai iya jan Sallah.


Kan hakan ne ɗaya daga ƴaƴan Marigayin Ahmad Ahmad Muhammad yayi ƙarin bayani kan haƙiƙanin abin da ke faruwa.


Ahmad ya kuma bayyana irin tsare-tsaren da suka yo domin inganta Masallacin, sannan ya bayyana dalilan da ya sanya ba su amince Dr. Indabawa ya zama Khalifa ba.


Malam Ahmad ya nuna damuwa kan kallon da jama'a suka riƙa yi musu ba tare da haƙƙi ba, sai don bayanan ƙarya da yace ana yaɗawa game dasu.


Ga ƙarin bayanin da yayi mana 👇👇

https://youtu.be/dRu9ozBh-RU

SOURCE, NASIRU SALISU ZANGO VIA FACEBOOK SEARCH. 
0 Response to "Ba zancen gadon Masallaci, so muke ayi tsari mai inganci don Dore war iyalan DR Ahmed buk. "

Post a Comment