--
An ceto mutane 6 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na edo.

An ceto mutane 6 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na edo.

>

An ceto mutane 6 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na edo.

Suna daga cikin mutane 31 da aka sace a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a tashar jirgin kasa da ke Igueben a karamar hukumar Igueben ta jihar. 

An ce wadanda lamarin ya rutsa da su na jira su shiga jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa Warri a jihar Delta. 

Amma kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na jihar Edo, Chris Nehikhare, a wani karin bayani game da harin a ranar Litinin, ya ce an ceto wasu daga cikin wadanda aka sace. Kamar yadda alkalumman wani binciken ya nuna; wadanda aka ceto sun hada da wata uwa mai shayarwa, jaririnta, da kuma wani yaro dan shekara 6.

Source, Rahama Tv via Facebook search. 

0 Response to "An ceto mutane 6 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na edo."

Post a Comment