--
RA'AYI: Wannan Ne Zai Tabbatar Da Cewa Ba Al'ummar Jihar Zamfara Ba Ne A Gaban Gwamna Matawalle Ba

RA'AYI: Wannan Ne Zai Tabbatar Da Cewa Ba Al'ummar Jihar Zamfara Ba Ne A Gaban Gwamna Matawalle Ba

>

 
RA'AYI: Wannan Ne Zai Tabbatar Da Cewa Ba Al'ummar Jihar Zamfara Ba Ne A Gaban Gwamna Matawalle Ba


Daga Ikra Lawali Bamamu Tsafe


Yayin da 'yan ta'adda ke cin karennsu ba Babbaka, suna kashe al'ummar jihar Zamfara tare da korar su daga gidajensu, a lokacin da yake cire makudan kudin al'ummar jihar yana gayyato 'yan fim domin biyan bukatarsa. 

 

Wannan ya zama wajibi mu fito mu gayawa al'ummar jihar gaskiya, da duk dan jihar Zamfara da ya sake kuskuren zaben Bello Matawalle a matsayin Gwamna, to Wallahi zai yi da na sani fiye da ta yanzu, kuma jihar Zamfara za ta shiga yanayin da ya fi wannan. Saboda ya zama wajibi gare mu mu fito mu fadawa al'ummar jihar Zamfara wannan gaskiyar. 


Alkawurra da ya yi kafin ya zama Gwamna babu wanda ya cika. Bayan kullum Jihar mu kara ci baya take yi ta kowane bangare, har ta kai ga talakawan Zamfara ba su son komai ga Gwamnati idan ba tsaro ba, amma hakan ya kasa samuwa. Kuma babu wani single protect da Gwamnan ya yi tunda aka rantsar da shi har zuwa yau. Ni ban san shi ba, ban kuma san wanda ya san shi ba.


Shin don Allah haka ake mulkin dimokradiyya ne? 


Kuma har wannan Gwamna zai iya fitowa ya ce yanabson a sake zaben shi karo na biyu. Tor me ya manto a fadar gwamnati da yake so ya je ya dauko?


A karshe ina kira ga al'ummar Jihar Zamfara da su sani cewa su yi hankali da sake zaben irin wannan gwamnatin da babu komai cikin ta bayan wahalar da talakawa ke ciki.


Daga Hon Ikra Lawali Bamamu Tsafe Local Government Zamfara State


Source /CREDIT /Rariya on Facebook search. 

0 Response to "RA'AYI: Wannan Ne Zai Tabbatar Da Cewa Ba Al'ummar Jihar Zamfara Ba Ne A Gaban Gwamna Matawalle Ba"

Post a Comment