--
Majalisar Dattijai ga CBN: Ku yi gyara a kan dokar ƙaiyade cire kuɗi

Majalisar Dattijai ga CBN: Ku yi gyara a kan dokar ƙaiyade cire kuɗi

>

 


Majalisar Dattijai ga CBN: Ku yi gyara a kan dokar ƙaiyade cire kuɗi 


Majalisar dattijai ta bukaci babban bankin Najeriya, CBN, da ya “gyara manufofinsa na takaita fitar da kudade duba da koke-koke da jama’a ke yi na nuna adawa da matakin.


Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa babban bankin kasar ya fitar da wata umarni na takaita fitar da kuɗaɗe zuwa N20,000 a duk rana a POS da kuma N100,000 duk mako ga ɗaiɗaikun mutane.


Manufofin sun tanadi cire N500,000 ga kungiyoyi da kamfanoni a duk mako.


Bayan yin la’akari da amincewa da shawarwarin da aka bayar kan kayyade kudaden da babban bankin na CBN ya yi a baya-bayan nan, a ranar Laraba, majalisar ta bukaci babban bankin da ya sake duba a kan tsarin.


Yayin da take dogaro da rahoton kwamitinta kan Bankuna, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, Majalisar Dattawa ta kuma umurci kwamitin da ya “ci gaba da sa ido kan babban bankin a kan kudirinsa na daidaitawa da ka’idojin cire kudi da kuma bayar da rahoton lokaci-lokaci ga Majalisar”.


Majalisar dattijai ta kuma kuduri aniyar, "goya wa CBN baya wajen ci gaba da aiwatar da ayyuka da ƙudirorinsa yadda ya dace da dokar bankin."Source /credit /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Majalisar Dattijai ga CBN: Ku yi gyara a kan dokar ƙaiyade cire kuɗi "

Post a Comment