--
Mangal Yana gina Katafaren Kamfanin Siminti Wanda zai Zama Shine na Biyu a faɗin Najeriya...

Mangal Yana gina Katafaren Kamfanin Siminti Wanda zai Zama Shine na Biyu a faɗin Najeriya...

>

 
Image Source /credit /Rariya Hausa via FacebookAlhaji Dahiru Yana gina Katafaren Kamfanin Siminti Wanda zai Zama Shine na Biyu a faɗin Najeriya...


Daga Falalu Lawal Katsina 


Babban Hamshaƙin ɗan Kasuwar Jahar Katsina Kuma Shugaban kamfanin jiragen Sama Na MAX AIR Alhaji Dahiru Barau Mangal Yana kan Aikin Babban Kamfanin sa na Siminti A garin Ayetoro Gbede dake cikin karamar kukumar Ijumu a Jihar Kogi...


A cikin Kamfanin an samar da filin tashi da sabkar jiragen sama da gidajen Ma'aikatan kamfanin da kuma asibiti tare ofishin yan sanda (Police Station), da kuma bangaren Bankuna domin jin daɗin abokan Huɗɗa .


Tuni dai Wannan aiki yayi Nisa Kuma Ana Tafiyar dashi Cikin Kwanciyar Hankali kuma ana Kyautata zaton Nan da Shekarar 2024 wannan Shiminta zai Karaɗe Ko Ina a faɗin Najeriya..An Bayyana Cewa Kamfanin zai rinƙa samar da Tan dubu shidda a kowace rana (6,000 Tones)...


Allah Ya tabbar talakawa da alkhairin dake cikin Wannan kamfani..Source /credit /Rariya Hausa via Facebook. 

0 Response to "Mangal Yana gina Katafaren Kamfanin Siminti Wanda zai Zama Shine na Biyu a faɗin Najeriya..."

Post a Comment