--
Gidauniyar AA Zaura Ta Ƙaddamar Da Bayar Da Magani Kyauta.

Gidauniyar AA Zaura Ta Ƙaddamar Da Bayar Da Magani Kyauta.

>

 Images Source /credit/ Rariya Hausa via Facebook. 


Gidauniyar AA Zaura Ta Ƙaddamar Da Bayar Da Magani Kyauta.


Shirin Samar da lafia ga kowa (ZH4ALL) na Gidauniyar A.A Zaura wato "A.A Zaura Foundation" a turance ta ƙaddamar da rabon magunguna da kuma kula da masu ciwukan da suka addabi al'umma.


Jagoran shirin na ZH4ALL Dakta Khalid Sunusi Kani yace Manufar wannan shirin shine ya zagaya ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, ya kuma samar da sauƙi ga ƙanana da matsakaitan ciwuka dake damun al'umma musamman mazauna karkara, ciwuka kamar; zazzabin cizon Sauro, hawan jini, ciwon suga, cututtukan da suka danganci haƙori da dai sauran cututtukan dake damun jama'a.


Kamar yadda kuke gani a wannan ƙaddamarwar, sama da mutane 500 ne suka amfana da wannan ƙaddamarwar wajen basu magungunan ciwukan da muka lissafa a sama, tare da wasu ɗimbim mutane da aka bawa shawarar lafiya. Sannan ta bawa sama da guda 400 gidan sauro domin kariya daga cutar cizon sauro 'malaria'.


A nasa jawabin mai gidauniyar ta AA Zaura, His Excellency Abdulkarim Abdussalam Zaura ya jaddada cewa game da cigaba da taimakon al'umma aiki ne da ya ɗauka wajibi a kansa, kuma babu ɗaga ƙafa, ya kara da cewar nan bada jimawa ba wannan shirin zai karaɗe faɗin Kano gaba ɗayanta, kamar yadda wasu ɓangarori na gidauniyar suka riga suka karaɗe jihar.


Waɗanda suka anfana dai tuni suke ta alasan-barka da addu'oi ga A.A Zaura don samun babar damar da abubuwan alheri zasu kara samuwa garesu.


Idan dai ba a mantaba a kwanakin baya ne A.A Zaura Foundation ta bada tiransformomi ga wasu garuwa don sama musu sauƙin wutar lantarki


#zauraproject4senatekanocentral


Source/credit /Rariya Hausa via Facebook. 

0 Response to "Gidauniyar AA Zaura Ta Ƙaddamar Da Bayar Da Magani Kyauta."

Post a Comment