--
Idan kuna son auren ku yayi gaggawar mutuwa to kubi wadannan hanyoyin

Idan kuna son auren ku yayi gaggawar mutuwa to kubi wadannan hanyoyin

>

 


Image Source /credit /Facebook 

#SIRRIN #KAWAYEN DA SUKE KASHE #AURE:

             

     

"kawayen da suke kashe aure-


babu shakka dole ne kowane mutum ya zama yana da mutanen daya amincewa da su a rayuwa kamar yadda ango yake da abokai haka ma matar take da kawaye wadanda ta amince dasu amma wani lokaci irin wadannan kawaye ne ke cin amanar ma'auratan har ta kai sun kashe musu aure.


  Wasu daga cikin kawayen amarya da abokan ango sun san abin da suke yi, kuma soyayyar da suke nuna wa ango da amarya ta Allah da annabi ce. Amma wasu babu abin da suke kudurce a zuciyarsu sai bakin-ciki da tsarku da tsuguma

 wasu ma kawayen daga bisani amarya take gamuwa dasu bayan ta tare a gidanta masu kananan shekaru da 'yan mata masu zuwa hira da kallon fina-final da matan aure ma kwabta da masu sayarda kayayyaki iri-iri da kuma dattijal da tsofaffi masu zuwa hira tare da yin gulmace-gulmace.


   Idan akayi rashin sa'a aka samun amarya ba mai nisan tunani bace, sai irin wadannan kawaye su fara kawo mata maganganu iri-iri har wani lokaci su rika gaya mata cewa al sun ga mijinta da wance ko kuma sun gan shi a wurin kaza.


  ita kuma daga nan sai ta hau kan abin da aka fada mata ba tare da tayi bincike ba ta fushi tana zare idanu tana cika tana batsewa, shi kuma angon ya rasa laifin daya yi mata ta haka shi ma idan ba mai nisan tunani bane sai yayi zuciya shi ma ya rika yin fushi ya rinka daure mata fuska daga nan sai alaka ta laace a fara kai kashedi wurin iyaye da waliyyan da suka daura auren..


   Idan kuwa akayi sa'a amaryar ko angon masu zurfin tunani ne zaka ga irin wadannan miyagun kawaye ba zasu ci nasara a kan suba saboda sun san duk gutsuri-tsomar da suka kawo musu ba zasu yarda da ita ba, balantana ma su amince da gulmace-gulmacen da ake yadawa a tsakaninsu

   amaren da suke da kulaficin kawaye wadanda duk wacce suka gani sai suyi kawace da ita su jawo ta jika ba tare da tantancewa ba, sune suka fi fadawa cikin wannan tarkon don ba kasafai namiji ya fiye yin abota mai zurfi ba kamar mace su mata suna da saurin yarda da amince wa juna irin amaren da suke tara kawaye a gidajensu babu shakka suna cikin hadarin fadawa tarkon gulma da yamadidi, kuma idan basu yi hattara ba alakansu da mazajensu na ciki hadari....


 Akwai wacce data tara kawayenta sai kaji ta saki baki a kwashe duk abin daya gudana tsakaninta da mijinta ta fada musu su kuma suyi ta dariya


  wasu da suke jin haushin ta a cikinsu sai su kuma su kwashe su gaya wa mijin ko yan'uwansa.


 Daga nan sai fara rikici maza a dinga sa ido ga kawaye 


idan kuma kaki wai baka so ka shiga harka ta 


 wata rana zaka samu matarka tana LESBIAN MADIGO 


  Allah ya kyauta a dinga sa ido

 mata a dinga kulawa.


 - wasu kawayen kuwa sai suyi amfani da abin da sukaji daga amaryar suyi kule-kullen da zasu yi su hada alaka da mijinta suja hankalinsa ta dabara suyi tayi mata sharri har ya sake ta su kuma su aure shi.


  nasan wannan ya faru da yawa ba sai an kawo misali ba.


  wasu kawayen ma irin matan nan ne da suke kashe aurensu sai su dawo su tare a gidajen amare suyi ta kulle-kulle har sai sun ga sun kashe wa duk amaryar da suka hadu da ita aure 

  zakaji suna yiwa amaren karyar cewa auren dole akayi musu ba kaunar mazan da suka aura sukeyi ba, ko kaji suna gaya mata cewa sai ta tashi tsaye idan ba haka ba uwar mijinta da 'yan uwansa zasu hana ta jin dadin aure kuma suce mata sai ta tashi tsaye ta nemi maganin da zata mallake mijinta daga nan sai su sanya ta a hanyar bin BOKAYE DA 'YAN BORI


SABODA HAKA MATA A DINGA KULAWA 


uwar gida ba zaki taba mallake mijinki ba


- sai kin kyautata masa

- sai kin basa hakkin sa

- sai kin kula da damuwar sa

- sai kin iya girki mai dadi

- sai kin iya kwalliya

- sai kin iya magana

- sai kin iya kwarkwasa

- sai kin iya mallake zuciyar sa da komai uwar gida


 ba zaka ta ba iya mallake zuciyar matarka ba


- sai kayi hakuri

- sai ka iya wanka 

wanka sa kaya turare da kwalliya

- sai ka iya magana

- sai ka iya soyayya maza da dama basa iya cewa mata I LOVE U daure ka fadi idan ka kasa zakaga wani yace mata 

- ka dinga neman shawarar ta

- ka dinga bata lokacinta

- ka dinga biya mata hakkin ta

- ka dinga wasa da ita

- ka dinga cin abinci ta

- ka dinga gode mata

- ka dinga neman shawarar ta

- ka dinga mata murmushi

- ka dinga mata komai na rayuwa idan bai fi karfi kaba

- ka dinga mata text messege na soyayya

- idan har ka kiyaye wannan zaka more rayuwar ka na aure mai gida


Source/credit/sirrin rike miji on Facebook 

0 Response to "Idan kuna son auren ku yayi gaggawar mutuwa to kubi wadannan hanyoyin"

Post a Comment