--
Dokar takaita cirar kuɗi ba don taimaka wa APC a zaɓen 2023 ba ne, CBN ya faɗa wa majalisar wakilai

Dokar takaita cirar kuɗi ba don taimaka wa APC a zaɓen 2023 ba ne, CBN ya faɗa wa majalisar wakilai

>

 Dokar takaita cirar kuɗi ba don taimaka wa APC a zaɓen 2023 ba ne, CBN ya faɗa wa majalisar wakilai


Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce manufarsa ta kayyade yawan kudaden da za a riƙa cire wa a banki ba don siyasa ba ne, sabanin zarge-zargen da ake yi.


Aisha Ahmad, mataimakiyar gwamnan CBN, ta bayyana haka a Abuja a yau Alhamis lokacin da ta ke amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar a zauren majalisar wakilai yayin zaman majalisar.


Misis Ahmad, wacce ta wakilci gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, ta ce manufar ta zo ne bayan tunani da bincike mai zurfi.


Ta yi wannan tsokaci ne ga tambayar da Chinedu Obidigwe (APGA-Anambra) ya yi ma ta, wanda ke son sanin ko manufar tana da nufin fifita jam’iyyar APC a zaben 2023.


Ahmad ta ce bankin na CBN ya bayar da umarnin a buga Naira biliyan 500 domin zagaya wa cikin al'umma, inda ta ce bankin ya yi sassauci ta hanyar duba manufofin cire kuɗi sama da Naira 100,000 zuwa Naira 500,000 ga daidaikun mutane da kuma daga Naira 500,000 zuwa Naira miliyan 5 ga kamfanoni. .


Ta ce ana sa ran manufar za ta samar da sabbin guraben ayyukan yi a bangaren fasahar sadarwa, sabanin yadda ake ta yada jita-jita cewa za ta kai ga rasa ayyukan yi.


Ta ce manufar ba za ta shafi masu gudanar da kamfanin na Point on Sales, POS, inda ta ce CBN na sane da cewa POS din ya samar da hanyar rayuwa ga ‘yan Najeriya kimanin miliyan 44.


Ahmad ta sha tambayoyi da ga ƴan majalisar da su ka yi tambayoyi masu da dama a kan sabon tsarin kudi.


Femi Gbajabiamila, shugaban majalisar, ya ce dalilin da ya sa ya kamata a yi wa majalisar bayani a kan irin wadannan manufofin shi ne, ‘yan majalisar su wakilai ne na wakilci jama’a.


Ya kara da cewa duk da cewa sake fasalin naira na iya zama kyakkyawar niyya, amma ya zama dole babban bankin ya dauki ‘yan majalisar.


SOURCE/CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Dokar takaita cirar kuɗi ba don taimaka wa APC a zaɓen 2023 ba ne, CBN ya faɗa wa majalisar wakilai"

Post a Comment