--
Ƴan takarar gwamna mata 25 sun bayyana ajandar zaben 2023

Ƴan takarar gwamna mata 25 sun bayyana ajandar zaben 2023

>

 

Ƴan takarar gwamna mata 25 sun bayyana ajandar zaben 2023


Gabanin zaben 2023, kimanin ƴan takarar gwamna mata 25 da suka fito takara a jam’iyyun siyasa daban-daban na jihohin kasar, a jiya Litinin, sun bayyana shirinsu na zaben.


Sun yi magana ne a wani taron manema labarai da Women Radio 91.7FM ta shirya a Abuja.


Matan Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Canada ne suka tallafa wa shirin.


A shirin, dukka ƴan takarar sun nuna gazawar maza gwamnoni a jihohin su.


Sun kuma ci alwashin cewa muddin aka zaɓe su a 2023 to fa sai sun kere maza wajen yi wa jihohi ayyukan ci gaba.


Ƴar takarar gwamna a jam’iyyar Action People’s Party, APP, a Delta, Annabel Cosmos, ta ce tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a 1999, mazan ba su yi abin da ya dace ba wajen baiwa jihar gyara fuska, don haka akwai bukatar mata su tashi tsaye wajen ganin sun fuskanci kalubale.


“Sun ce abin da namiji zai iya yi, mace za ta iya yi.


“Kada a bar mata a dakin girki. Dakin girki ba wurinmu bane; za mu iya mulkin jihar idan aka ba mu dama.mu yi hidima,” inji ta.


Ta ce idan aka zabe ta gwamna za ta duba fannin ilimi, noma da kiwon lafiya da dai sauransu, da nufin kawo sauyi.


Haka sauna sauran ƴan takarar sun ci alwashin kawo ci gaba a jihohin su idan aka zaɓe su.SOURCE /CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Ƴan takarar gwamna mata 25 sun bayyana ajandar zaben 2023"

Post a Comment