--
Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru da dala biliyan 1.5 a watan Nuwamba

Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru da dala biliyan 1.5 a watan Nuwamba

>

 Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru da dala biliyan 1.5 a watan Nuwamba


Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya samu ƙaruwar dala biliyan 1.5 a cikin dukiyarsa a watan da ya gabata na Nuwamba, bayan da ya samu dala miliyan 200 a watan Oktoba. A halin yanzu dukiyarsa ta kai dala biliyan 19.1, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 81 mafi arziki a duniya.


Rahoton Bloomberg Billionaires Index, wanda ke bin diddigin tare da kwatanta dukiyar mutane 500 mafi arziki a duniya, ya bayyana cewa dukiyar Dangote ta karu da dala biliyan 1.5 a watan Nuwamba, wanda ya mayar da asarar dala miliyan 611 a cikin watanni 10 na farko na 2022.


An danganta karuwar da hauhawar farashin hannayen jarin Dangote Cement Plc, wanda ya dawo da karfin tuwo bayan watanni da aka kwashe darajar hannun jarin na faɗuwa.


Aliko Dangote ya samu dimbin arzikinsa ne daga hannun jarin da kashi 86 na siminti na Dangote, wanda a halin yanzu ya kai dala biliyan 8.64.


Har ila yau, ana iya danganta karuwar arzikinsa da masana’antar takin sa, wacce ke iya samar da ton miliyan 2.8 na urea a shekara; ya na da darajar dala biliyan 5.


Da ƙaruwar dala biliyan daya da ya samu wanda ya kawar da asarar dukiyar da ya yi a duk shekara a farkon watan, dala miliyan 611, hamshakin attajirin na Najeriya ya bi sahun Abdul Samad Rabiu, wanda ya samu karuwar arzikinsa a bana. 


Idan dai za a iya tunawa, Aliko Dangote ya bayyana cewa sabon jarin da ya zuba zai samar da ayyukan yi akalla 300,000 a Nijeriya, yayin da ya ke ci gaba da saka hannun jarin da ya dace a harkar kasuwancin sa na sukari, daidai da ka’idojin da aka tanada na tsarin samar da suga a Nijeriya.


SOURCE /CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook. 

0 Response to "Arzikin Aliko Dangote ya ƙaru da dala biliyan 1.5 a watan Nuwamba"

Post a Comment