--
Qatar 2022: Saudiyya ta girgiza Argentina 2-1

Qatar 2022: Saudiyya ta girgiza Argentina 2-1

>

 

Qatar 2022: Saudiyya ta girgiza Argentina 2-1


Tawagar kwallon kafa ta Saudiya ta kafa tarihi a duniya, inda ta casa Argentina da kwallaye 2-1 a Gasar Cin Kofin Duniya da ke gudana a Qatar.


Argentina ce ta fara zura kwallo ta hannun Messi a bugun fenariti a minti na 10 da saka wasan.


Da ga bisani sai Saudiya ta farke ta hannun Saleh Al-Shehri a minti na 48, kafin Salem Al Dawsari ya kara ta biyu a minti na 53.


Tuni masharhanta suka bayyana wannan nasarar ta Saudiya a matsayin wani gagarumin al’amari da ya girgiza duniyar tamola.


Saudiya dai, ita ce kasa ta 51 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, yayin da Argentina ke matsayin na 3, sannan kuma ta taba lashe kofin duniyar har sau biyu.


Argentina na cikin manyan kasashen duniya da ake sa ran za su taka gagarumar rawa a yayin gasar ta cin kfin duniya a Qatar.


Source 👇

Daily Nigerian Hausa on the Facebook. 

0 Response to "Qatar 2022: Saudiyya ta girgiza Argentina 2-1"

Post a Comment