--
Na yi mafarki Peter Obi ya ci zaɓe -- Ƴar BBNAIJA, Mercy Eke

Na yi mafarki Peter Obi ya ci zaɓe -- Ƴar BBNAIJA, Mercy Eke

>

 
Na yi mafarki Peter Obi ya ci zaɓe -- Ƴar BBNAIJA, Mercy Eke


Wacce ta lashe gasar Big Brother Naija karo na 4, Mercy Eke, ta ce ta yi mafarkin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya lashe zaben 2023.


Ta bayyana hakan ne ta shafinta na Twitter a jiya Alhamis, inda ta kara da cewa burinta koyaushe ya na cika.


Ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “Na yi mafarki Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa a 2023. Kullum burina yana cika. Sabo da haka wannan mai yiwuwa ne. Za mu iya samun wannan nasarar. A bayyane ta ke PO zai iya lashe zabe, mu matsa da addu'a sosai. Mu na dab da sake gyaran mayar da Najeriya."


Ƴar shekaru 29, kuma daga jihar Imo, Eke yar jarida ce a Najeriya, ƴar wasan kwaikwayo, vixen na bidiyo kuma yar kasuwa.


Ta na goyon bayan Obi ne, wanda ke cikin manyan ‘yan takara a zaben shugaban kasa na 2023.

Source /credit 👉 Daily Nigerian Hausa on Facebook. 

0 Response to "Na yi mafarki Peter Obi ya ci zaɓe -- Ƴar BBNAIJA, Mercy Eke"

Post a Comment