--
Jami'an Tsaro Sun Kama Gaggan 'Yan Bindiga Masu Garkuwa Da Mutane 16 A Jihar Zamfara

Jami'an Tsaro Sun Kama Gaggan 'Yan Bindiga Masu Garkuwa Da Mutane 16 A Jihar Zamfara

>

Jami'an Tsaro Sun Kama Gaggan 'Yan Bindiga Masu Garkuwa Da Mutane 16 A Jihar Zamfara 


Daga Comr Abba Sani Pantami 


A cikin 'yan kwanakin da suka gabata hukumomin tsaro sun samu nasarar kashe daruruwan 'yan ta'addan da suka addabi jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Sokoto cikin wa 'yanda aka kashe akwai manya manyan 'yan ta'addan da suka addabi yankunan da suka hada da; Halilu Buzu, da Yellow Kano da Alaji Gana da kuma Kachalla wanda shi kuma a Kaduna aka kashe shi. 


Ya zama dole mu jinjinawa jami'an tsaron Najeriya da gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin mai girma gwamna Dr. Bello Matawalle bisa hadin kai da goyon baya da karfafa gwiwa da yake bawa jami'an tsaron don ganin sun kawo karshen 'yan ta'adda a yankunan baki daya. 


Sabon salon yaki da jami'an tsaron suke gudanarwa yana daga cikin dalilan samun wa 'yan nan manyan nasarorin da kuma Addu'o'in da muke musu.


Muna rokon Allah ya cigaba da bawa jami'an tsaron Najeriya Nasara. Allah ya zaunar mana da kasarmu lafiya.


SOURCE 👇

Fitila Hausa via Facebook. 

0 Response to "Jami'an Tsaro Sun Kama Gaggan 'Yan Bindiga Masu Garkuwa Da Mutane 16 A Jihar Zamfara "

Post a Comment