"Ina Hasashen Mutuwar APC bayan Zaɓen 2023" - Atiku AbubakarDan Takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi hasashen rugujewar jam’iyyar All Progressives Congress bayan zaben 2023.


Atiku ya fadi haka ne a yayin kaddamar da kungiyar yakin neman zaben PDP ta Matasa a Abuja, ranar Alhamis.


Dan takarar PDP ya ce, “Gaskiya PDP ce kadai jam’iyyar siyasa, APC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kawance ne tsakanin CPC da jam’iyyar Tinubu, kuma mun ga yadda kawance ya bace a kasar nan cikin dare.


“Bana tunanin APC za ta tsira bayan zaben nan, za mu kada kuri’a a zaben, kuma idan muka zabe su, za su mutu.”


SOURCE :RAHAMA TV FACEBOOK. 

0/Post a Comment/Comments