BAN TABA MALLAKAR GIDA A KASAR WAJE BA INJI SHUGABA MUHAMMAD BUHARI

 


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a lokacin ganawa da Sarki Charles na III, a fadar Buckingham ya shaida masa cewa ba shi da gida na kansa a Burtaniya.


A lokacin ganawa da 'yan jarida bayan ganawa da sarkin mai shekara 73, ya ce sarkin ya tambaye shi ne ko yana da gidan kansa a Burtaniya.


Buhari ya ce makusudin ziyarar ita ce tattaunawa kan alaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci da kuma diflomasiyya.


Ya ce an tsara ganawar ta su ne a baya a birnin Kigali tun kafin ya zama sarki, amma sai a wannan lokacin ne ganawar ta tabbata

Source : rahama tv Facebook. 

0/Post a Comment/Comments