--
Idan Mace Tana Maka Wadannan Tambayoyin Tanada Ra'ayinka Ne: (maana tana sonkane)

Idan Mace Tana Maka Wadannan Tambayoyin Tanada Ra'ayinka Ne: (maana tana sonkane)

>
Image source /credit / Facebook  Idan Mace Tana Maka Wadannan Tambayoyin Tanada Ra'ayinka Ne:


 

Mata sunada hanyoyinsu na nunawa namiji suna son shi ba tare da ta furtawa wanda take ra'ayi kalmar so ba.


Cikin hikima da dabaru da kuma alamu wasu matan ken furta kalaman so ga wanda ta kyasa.


Ga waau tambayoyin sai mace mai ra'ayinka kadai zata yi maka su.

 

1: Kana Da Budurwa?


Wannan shine tambayar farko da mace mai ra'ayinka zata soma neman amsar sa kamin ta saki jiki da kai.

Akasarin mata suna son jin namaji yace bai da budurwa ko kuma bai da mata. Hakan na basu kwarin gwaiwa wajen ganin sun cimma burinsu.


Sai dai kuma wasu matan sun fi so ka sanar dasu gaskiyar halin da kake ciki idan kana da budurwa ko mata. Don haka kada ka yiwa macen data nemi amsar wannan tambayar karya domin ka burgeta. 

Idan mace ce mai ra'ayinka tana iya hakura ta shiga takara da wannan budurwar da kake da ita , idan kuma bata ra'ayin soyayya da kai a hakan daga wannan lokacin zata hakura da kai. 


2: Aikin Me Kake Yi?


Shima wannan tambaya ce da mace mai ra'ayinka take son sanin amsarsa.

Da yake ita mace 'yar ayi mata ce. Zata sone taji idan har ta samu hadin kanka zaka iya kula da ita. Shi yasa zata so sannin abunda kake yi a rayuwa.

Kada ka mata karya saboda ka burgeta. Bata amsa na gaskiya muddin dai kana da ra'ayin ta kaima.


3: Mai Ya Rabaku Ko Mai Yasa Bakada Budurwa:?


Shima tambaya ne da mace mai kerkeranka take son jin amsar sa.

Idan kace mata bakada budurwa zata so sanin dalilin hakan. Idan kace kun rabu ko kun bata nan ma bazata barka haka ba sai ta nemi sanin dalili. 

Don haka idan kana raayinta kai ma bata amsa na gaskiya domin ganin baku samu matsala nan gaba ba.


4: Wani Irin Mace Kake So? 


Mace mai ra'ayinka zata maka wannan tambayar ne domin sanin ko zata samu wuri a zuciyarka.


Da zaran mace ta maka wannan tambayar tana sonka ne. Amsar da zaka bata kuma shi ne zai bata karfin gwaiwa ko kuma kashe mata gabobinta. 


5: Ko Zaka Koyardani Wannan Darasin?


Wannan salon neman shiga ne da mata dalibai suke yiwa maza dalibai da suke ra'ayinsu wannan tambayar.


Da zaran kaga budurwa ta nemi lokacinka domin ka nuna mata wasu darusa a makaranta kawai ra'ayinka take yi, musamman idan kasan wasu mazan da tafi kusanta dasu da zasu iya nuna mata.


#Tsangayarmalamtonga 

Waɗannan sune wasu alamun da mace zata nuna tana ra'ayinka amma ba tare da ta furta maka Kalma so ba.

Da fatan gayu zasu bada hadin kai.


SOURCE /CREDIT / sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Idan Mace Tana Maka Wadannan Tambayoyin Tanada Ra'ayinka Ne: (maana tana sonkane) "

Post a Comment