--
Duk mace mai hali irin wannan ta tsira duniya da lahira wallahi

Duk mace mai hali irin wannan ta tsira duniya da lahira wallahi

>

 Image source 👉Facebook 


Bayan ya lakaÉ—a mata duka, ya ci mutuncinta. Ta kalle shi ta ce: Zan je in kai Ć™ararka 


Ya ce: ba sai kin fita ba, babu in da zan barki ki je.


Ta tashi ta nufi banÉ—aki, ta yi alwala, ta fara Sallar Nafila, ta yi doguwar sujjada, tana addu'a. Bayan sallamewarta, sai ta sake É—aga hannu don ci gaba da addu'a.


Kwatsam Mijin ya riƙe hannayenta, yanzu duk ƙarar da ki ka kai a Sujjada bata isa ba sai kin sake ɗaga hannu. Don Allah ki yi haƙuri, wallahi duk abin da na aikata ya faru ne a cikin fushi, wallahi na yi miki alƙawarin ba zan sake ba.


Ta kalle shi cikin murmushi, ta ce: da ka ƙyale ni na cigaba da addu'a ta, wallahi tun da na sanya kaina a cikin Sujjada babu wani alheri face sai da na roƙi Allah ya baka.


Tare da duk abin da kake aikatawa, kai Mijina ne, kuma ina ƙaunarka sosai, ya za a yi na yi maka mummunar addu'a...!?


Source 👉sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Duk mace mai hali irin wannan ta tsira duniya da lahira wallahi "

Post a Comment