--
Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan Nijeriya

Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan Nijeriya

>

 Image source /credit /Daily Nigerian Hausa on Facebook. 


Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan Nijeriya


Babban hamshakin attajiri a Afrika, Aliko Dangote, na kyautata zaton cewa sabon saka hannun jari na biliyoyin nairori a ɓangaren sukari zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da ba zai yi kasa da dubu 300 ba a Nijeriya.


Sanarwar da Sashen Sadarwa na Kamfanin Aliko Dangote Group ya fitar ta ruwaito Dangote ɗin na cewa kamfanin na samar da sabbin hanyoyin samun kudade don haka ya fadada ayyukansa a bangaren sukari.


Dangote, wanda ke magana a wajen bikin bada lambar yabo ta shekarar 2022/2023 da aka yi a Numan, jihar Adamawa, ya ce damar da za ta samu za ta hada da ayyuka kai tsaye da kuma waɗanda ba na kai tsaye ba.


Dangote, wanda shi ne babban mai bayar da agaji a nahiyar Afirka, ya bayyana fatansa cewa dimbin jarin zai samar da ayyukan yi sama da 300,000 ga ƴan Nijeriya.


Ya ce, “Muna zuba jari mai yawa a jihar Adamawa ta hanyar fadada karfin tace sukari na DSR Numan daga 3000tcd zuwa 6000tcd, 9800tcd, zuwa 15,000tcd. 


"DSR zai iya ƙirƙirar ayyuka kusan dubu ɗari uku, kai tsaye da kuma wanda ba na kai tsaye ba, tare da ingantattun tasirin ninkawa kan tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya," in ji shi. source /credit /Daily Nigerian Hausa on Facebook. 

0 Response to "Dangote na shirin samar da sabbin ayyuka dubu 300 ga ƴan Nijeriya"

Post a Comment