--
Kyawun ki baya tasiri bayan aure matukar baki Zamo mai Kyawun hali ba,

Kyawun ki baya tasiri bayan aure matukar baki Zamo mai Kyawun hali ba,

>

 
Image source /credit /Facebook 


KYAWUN KI BA YA TASIRI BAYAN AURE MATUKAR BA KI ZAMO MAI KYAWUN HALI BA !


Shi kyawun mace yakan jawo namiji ya so ta so matuka, kuma yayi hakuri ya jure duk wahala ko kashe dukiya ya aure ta, amma daga karshe in zama yayi zama in ta zamo ba mai halayya ta gari ba, sai duk wannan soyayyar ya kare wani lokacin har ya kai ga rabuwa ya kasa hakuri !


Nasihar mu a yau gare ki shine ki zamo mace mai tsoron ALLAH ta gari, ko a yau kika samu mai qaunar ki ga kuma ke kyakkyawa kiyi kokari zamo wa mai kyawun hali, domin kyawun mace daga ɗa namiji ya aure ta to yana iya gushe wa a fuskar sa ba zai zamo mai tasiri ba, amma idan mace ta zamo mai kyawawan halaye to a kullum soyayyar ta na kara shiga zuciyar sa ne, kyawun ta ya zamo yana kyalkyali a ko da yaushe a idanun sa, kiyi amfani da soyayyar da yake miki wajen samun aljannah ta hanyar girmama shi da kiyaye hakkokin sa wannan ne zai tabbatar da ke a zuciyar sa, duk wani abu da zai kara muku kauna ko yake so kiyi shi matukar bai saɓawa ALLAH ba, ki kuma zamo mai addu'a !


Amma ki sani duk yadda kika kai ga kyau matukar baki da ɗa'a watarana dole ki rasa mijin ki, ko ki rasa hankalin sa, ko ki zamo kece wacce kika zamo soyayyar ki ba ta da tasiri a zuciyar !


Kiyi amfani da damar ki kici moriyar duniya ki kuma nemi lahira , ki zamo mai tsoron ALLAH da hakuri, idan kika riki wa'ennan za ki ji daɗin duniya kuma ki samu dacewa !


Rasheedah Bintul Islam


Source /credit /sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Kyawun ki baya tasiri bayan aure matukar baki Zamo mai Kyawun hali ba, "

Post a Comment