--
Akwai yuwuwar a yanke wa mawaki 442 shekaru shida a gidan yarin ƙasar Nijar.

Akwai yuwuwar a yanke wa mawaki 442 shekaru shida a gidan yarin ƙasar Nijar.

>

 







Akwai yuwuwar a yanke wa mawaki 442 shekaru shida a gidan yarin ƙasar Nijar.  


Kamar yadda rahotanni su ka bayyana wanda makusanciyar mawaki Mr 442, Murja Ibrahim Kunya ta bayyana a shafinta ta TikTok, mawaƙin da abokinsa Ola of Kano sun je ƙasar Nijar inda su ka yi ɓadda kama su ka je yin fasfotin fita ƙasa da ƙasa wato “International Passport.”


“Sanin kowa ne cewa in har mutum ba ɗan ƙasa bane, babban laifi ne yaje yin fasfo a ƙasar da ba tashi ba. Yayin da 442 da abokinsa su ka yi aski don su samu passport din zuwa kasashen da aka haramta wa ‘yan Najeriya zuwa, ta Nijar, sai aka yi ram dasu.


Yanzu haka an tasa ƙwayar su a gidan gyaran hali inda su ke jiran hukuncin da za a yanke musu. Akwai yuwuwar a yanke ko ko wannensu shekaru 6 a gidan yari cif-cif kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar akan duk ɗan ƙasarta.”


 Labarun Hausa.

SOURCE 👇

Hasken Shiriya on Facebook. 

0 Response to "Akwai yuwuwar a yanke wa mawaki 442 shekaru shida a gidan yarin ƙasar Nijar. "

Post a Comment