--
MAGANIN CIWON HAKORI    CIWON HAKORI

MAGANIN CIWON HAKORI CIWON HAKORI

>CIWON HAKORI


A Sami Itacen Tumfafiya A  Dafa Da Jar Kanwa a Kuskura   da Dimin Shi Safe da Yamma Har Kwana 3,

 Haqora Zaa Warke,


KOGON HAKORI


A dibi Audugar Cikin Kwallon Tumfafiya a Dangwali Nonon ta Kadan a Sa Cikin Kogon, A Riqa Yin Haka Lokaci-Lokaci, Kogon Zai Cike, (Amma fa Akwai Zafi)


TSUTSAR HAKORI


A  Tafasa Saiwar Tumfay a Kuskura da Dimin Shi, Sau 3 A Rana Kwana 2,

Zaka Rabu da Ita,,


HAKORA MAI JINI


A Dafa Sassaqen Tumfafiya da Ganyen ta A Sa Gishiri Kadan, A Kuskura Baki da Dumi-Dumi Sau 3 A Rana Kwan 1 Zaayi,

Haqora Za Su Daina Jini


WARIN BAKI

A Dafa Furen Tumfafiya da Kwallon Ta Idan Ruwan Ya Huce A Sa A bin Wanke Baki (Brush)  Ana Wanke Bakin Bayan an Dan Guntsi Ruwan

Kayi Ban Kwana da Doyin Baki,


HASKEN HAKORA


A Shanya Furen Tumfafiya Idan Ya Bushe A Maida Shi Gari A Hada Shi da Alif Kadan, A Dan Gwala da Buroshi ko Asuwaki A Wanke Baki,

Hakora Za suyi Fari Tas,


DATTIN GORO KO HAYAKIN TABA

A Dafa Furen Tumfafiya da Lemun Tsami (Lime) A Wanke Baki Dashi da a bin Wanke Baki (Brush)

Dattin Zai Fita Daga Baki Gaba daya


Source 👇


Faruqu Faruqu on Facebook. 


0 Response to "MAGANIN CIWON HAKORI CIWON HAKORI"

Post a Comment