--
2023: Ba za mu ƙyale duk wani ɗan siyasa da ya haɗa rikicin zaɓe ba -- NSA

2023: Ba za mu ƙyale duk wani ɗan siyasa da ya haɗa rikicin zaɓe ba -- NSA

>

 


Babagana Monguno, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya ce za a yi maganin ƴan siyasan da ke shirin kawo cikas a zabe mai zuwa.


Monguno ya yi wannan gargadin ne a yau Juma’a a wani taron gaggawa na tsaro da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya.


INEC ta shirya taron na gaggawar ne bayan da aka kone ofishin ta a jihohin Ogun da Osun.


Bayan haka, sai aka haɗa taron gaggawa da mambobin kwamitin tuntuba na hukumomi kan harkokin zabe biyo bayan afkuwar lamarin.


Da ya ke jawabi a wajen taron, Monguno ya ce ya na sane da cewa a cikin watan da ya gabata, an samu rahoton tashin hankalin zabe akalla 52 a jihohi 22 na Nijeriya.


Ya bayyana lamarin a matsayin mummunar manuniya wacce dole ne a tashi tsaye a kai.


“Dukkanmu muna sane da cewa shugaban kasa, a kan kansa, ya himmatu wajen tabbatar da kare dimokradiyya. Wannan shi ne abin da mutane ke so,” in ji NSA.


“Shugaban ya kuma ba da umarninsa ta hannu na ga dukkan jami’an tsaro na sirri da sauran jami’an tsaro da su tabbatar da cewa an gudanar da zaben 2023 cikin yanayi na zaman lafiya ba tare da rikici ba.


“Shugaban kasa ya yi matukar farin ciki da sakamakon zaben Anambra, Ekiti, da Osun kuma yana son a sake yin irin wannan a 2023 - wata alama ce ta jama’a za su yi nasara a kan duk wani cikas da ka iya wargaza dimokradiyyar da muke kokarin karewa.


SOURCE : DAILY NIGERIAN HAUSA FACEBOOK. 

0 Response to "2023: Ba za mu ƙyale duk wani ɗan siyasa da ya haɗa rikicin zaɓe ba -- NSA"

Post a Comment