--
Allah sarki mata: Tabbas Jinkirin Aure Jarabawa Ne Daga Allah

Allah sarki mata: Tabbas Jinkirin Aure Jarabawa Ne Daga Allah

>


Tabbas Jinkirin Aure Jarabawa Ne Daga Allah


Duk kusancinka da alaƙarka da mace kar ka tambayeta cewa: 


• Yaushe za ki yi aure?

• Ba ki yi aure ba har yanzu?


Irin waɗannan tambayoyin, akwai waɗanda saboda da takaici da ciwo, har kuka suke in sun shiga ɗaki. Kai ba zaka gane irin raɗaɗin da suke ji a ransu ba. 


Kamar kai ne ka gamu da jarrabawar SPILLOVER a jami'a, shekaru 2 kana zuwa gyara; wani ya tambayeka cewa, "ME YA SA HAR YANZU BAKA YI GRADUATION BA?" 


AURE a karan-kansa, ba kan kowa ya wajaba ba, matuƙar ba zaka afkawa alfasha ba. Akwai waɗanda aure ya zame musu wajibi, wasu mustababbi (abin so), wasu makruhi, wasu ma haramun ne a kansu su yi auren. Wannan ƙa'idar tana hawa kan kowanne jinsi, 'namiji' ko 'mace' [Fiqh Al-Sunnah, 2/15].


AURE BABBAR NASARA CE A RAYUWA, MUSAMMA GA 'YA MACE. Amma babu inda addini ya ce, in mace ba ta yi aure ba, ta zama 'wata mai laifi' ko in ta mutu bata yi aure ba zata shiga 'Aljanna' ba. Ba laifi ba ne ina mace ta zauna ba aure, matukar zata kiyaye mutuncinta.


A al'adarmu ake ganin, in mace bata yi aure ba, tamkar wani LAIFI ta aikita, ko a cikin gidaje, a gaban iyayenta, a yi ta tsangwama mata, kullum a cikin takaici.


DAGA Aliyu M. Ahmad

0 Response to "Allah sarki mata: Tabbas Jinkirin Aure Jarabawa Ne Daga Allah"

Post a Comment