--
Duk Mai Imani Wannan Videon Zai Girgiza masa Zuciya..Kalli Yanda Pantami Keyiwa Wata Dattijuwa Addu'a Gaskiya Wannan Addu'ar Samun Tsawon Rai da Haduwa a Aljannah.

Duk Mai Imani Wannan Videon Zai Girgiza masa Zuciya..Kalli Yanda Pantami Keyiwa Wata Dattijuwa Addu'a Gaskiya Wannan Addu'ar Samun Tsawon Rai da Haduwa a Aljannah.

>


 SABAWA IYAYE DA MUMMUNAN SAKAMAKONSA, ALLAH YA TSARE MU


Kishiyar biyayya ga iyaye shi ne saba musu. Wannan mummunan hali ne , babban zunubi ne da yake janyo tsinuwar Allah da mummunan karshe a duniya da lahira. Allah ya kiyaye mu. 


Hanyoyin sabawa iyaye suna da yawa, kadan daga cikinsu sune:

Sanya iyaye kuka da bata musu rai da jawo musu bakin ciki.



1. Kosawa da yi musu hidima, da yi musu kwafa ko tsaki, ko hayaniya, ko daka musu tsawa, ko daure fuska da harara a gare su, da nuna damuwa da gajiya da su.


2. Raina su da kin girmama su da wulakanta su.


3. Zaginsu ko jawo musu zagi.


4. Kushe su da aibata su da gwale su, da sifanta su da jahilci, dakikanci, rashin wayewa da rashin tsari. Haka kushe girkin uwa da kyankyaminsu musamman bayan sun tsufa ko kuma ba su da lafiya,da raina su don kawai su talakawa ne.


5. Ba su umarni musamman saboda da yana da kudi da daka musu tsawa.


6. Nauyin jiki wajen hidimta musu da ja musu rai da yi musu alkawari ba cikawa da kin gaggauta biya musu bukatunsu.


7. Kin sauraron su da katse su idan suna magana.


8. Yi musu rowa da dan hannu wato kwauro da lissafa musu abinda ka yi musu da nuna musu ai ba don kai ba da sun shiga uku da makamancin haka.


9. Kin dawowa gida da wuri alhali suna da bukatar ka, ko yin tafiya ba tare da izininsu ba, ko dadewa ba ka ziyarce su ba, kana can kana gararin duniya.


10. Yasar da su a gidan tsofaffi kamar yadda ake yi a wasu kasashen ko barin su a kauye ko lungu suna cikin rubabben gida kai kuma kana cikin birin ko (GRA) cikin kerarren gida kai da matarka kuna cin duniyarku da tsinke ,su kuwa suna kwana cikin annakiya da tsummokara tare da beraye da jaba da sauran kwari.


Idan ma ba za ka fito da su cikin birni ba,to ka kere musu gidan lungun ko kauyen.


11. Fatan rabuwa da su saboda ka gaji da wahala da su.


12. Fifita matarka da `ya`yanka da surukanka da abokanka a kansu.


13. Yawan tashin hankali tsakaninka da `yan`uwanka ko iyalinka wanda zai rinka jefa su cikin damuwa,da shiga cikin rigingimun da za su jefa su cikin zulumi da damuwa.


14. Yawan mita da kukan babu a gabansu don ma kada su sa rai da abin hannunka.


15. Jin kunyar danganta kanka da su saboda talaucinsu ko wata lalura ko wani hali da suke da shi.


16. Yi musu girman kai da dagawa da jin cewa yanzu fa sai dai su su bi ka amma ba wai kai ka bi su ba saboda wani matsayi da ka samu na ililmi,ko wadata,ko mulki.


17. Nuna musu kiyayya da rashin tausayi.


18. Kin yin biyayya ga `yan`uwansu da abokansu da kawayensu.


19. Kin yi musu addu'a da sadaka da kin biya musu bashi bayan mutuwarsu.


A takaice dai duk abinda zai bata musu rai mutukar ba bin Allah ba ne, shi ne sabawa iyaye. A kula!


MUMMUNAN SAKAMAKON SABAWA IYAYE


 Bayan sabawa Allah Ta'ala da Manzonsa sallallahu alaihi wasallam babu zunubin da ya kai girma da munin sabawa iyaye. 

Kuma tun daga duniya mai sabawa iyaye zai fara shiga halin takaici da nadama kafin ya je lahira.


Ga kadan daga mummunan sakamakon masu sabawa iyayensu :


(1) Allah Ta'ala da Manzonsa suna fushi da su.

(2) Allah yana gaggauta saukar da azaba da musiba a kansu.

(3) Rayuwarsu da arzikinsu ba sa yin albarka.

(4) Yadda suka yi wa iyayensu sai `ya`yansu sun yi musu har ma da kari.

(5) Ba za su shiga aljanna ba.

(6) Duk inda suke rahama ba ta sauka.

(7) Bayansu ba ta yin kyau.

(8) Allah ba ya karbar ayyukansu na alhairi.

(9) Ba su da kima da mutunci a idon mutane.

(10) Karshensu ba ya yin kyau.

(11) Ba sa samun sauki a kabarinsu.

(12) A lahira za su gamu da matsananciyar azaba.


Ya Allah ka shiryi masu sabawa iyayensu su daina su je su nemi afuwarsu da yardarsu tun kafin su rabu suna masu fushi da su. Amin.


SHIN ME YA SA AKE SABAWA IYAYE ?


A halin yanzu da dama daga cikin iyaye sun koma kamar su ne `ya`yan su suke bin `ya`yan suna lallaba su suna neman yardarsu, ba sa saba umarninsu, akan su sai su iya batawa da kowa, amma duk da haka `ya`yan suna matukar bata musu, ba sa bin su ba sa tausaya musu.

To shin wane dalili ne yake kawo hakan?


Akwai dalilai da dama akan haka, wadansu daga iyayen ne, su kansu, wadansu daga `ya`yan, wadansu daga yanayin al'ummar gari.

Kadan daga cikin wadannan dalilai sune:


1. Rashin tarbiyyar iyaye da jahilcinsu ga addininsu. Da kuma rashin sanin yadda ake yin tarbiyyar `ya`ya a Musulunci.

2. Zaluncin iyaye na kin sauke hakkokin `ya`yansu da Allah ya dora musu, musamman na tarbiyya.

3. Nuna bambanci tsakanin `ya`ya da fifita wadansu akan wadansu.

4. Wulakanta 'ya'ya da rashin girmama fahimtarsu da kin shawarartarsu akan abinda ya shafe su musamman in sun fara hankali da fahimtar rayuwa ,da kin  jan su a jiki, sai ka ga da  ya shekara arba'in amma ana har yanzu ana gwale shi ana ce masa   yaro mara hankali, ba a  yin komai da shi musamman in ba shi kudi.

5. Shagwaba `ya`ya da sangarta su da kin kwabarsu da jin haushin duk wanda zai ce su gyara halinsu.

6. Rashin nagartar iyaye ta yadda ``yaya ba su da wani abu da za su kwaikwaya mai kyau daga iyayensu, su kansu ba su bi nasu iyayen ba, ba su kyautata musu ba, ballantana a bi su.

7. Tasirin kallace-kallace da karance-karance na finafinai da littattafai na rusa tarbiyya da tsotse imani a wayoyi da talabijin da sauran hanyoyin sadarwa na zamani.

Jahilcin `ya`ya na rashin sanin hakkokin da iyayensu suke da su a kansu.

8. Tsananin son abin duniya. A yanzu babu mai daraja a wurin mafi yawancin `ya`ya sai mai kudi.

9. Rashin damuwar mutane da tarbiyyar `ya`yansu da na `yan`uwansu. A da ana cewa "da na kowa ne" amma a yanzu maganar ta koma "da na mai shi ne kawai".


A dunkule wadannan su ne dalilan da suke sa `ya`ya su sabawa iyayensu, su bujire musu su ki kula da su. 


Sai mu yi cikakken nazari a tsanake mu gyara da kanmu.


INA MAFITA?


Mafita anan a takaice ita ce tun kafin aure mutum ya dage ya nemi ilimi ya san yaya ake neman aure? Yaya ake zaman aure? Wadanne  hakkoki ne suke kan ma'aurata?


Idan an samu ciki yaya ake yin goyon ciki? Yaya ake kula da mai ciki? Wadanne hakkoki iyaye suke da su akan `yayansu? Yaya ake yin tarbiyyar `yaya a duk bangarori da matakan rayuwar yaya?


Bayan an san haka sai kuma a yi aiki da sanin.


Da yardar Allah wannan zai magance mana matsalolin rashin tarbiyya da sabawa iyaye da kangare musu.


Allah ka datar da mu zuwa ga dukkannin alhairai.


Daga littafi na mai suna 

"Hadisai 40 kan falalar bin iyaye da sadar da zumunta."

5/2/2022.

0 Response to "Duk Mai Imani Wannan Videon Zai Girgiza masa Zuciya..Kalli Yanda Pantami Keyiwa Wata Dattijuwa Addu'a Gaskiya Wannan Addu'ar Samun Tsawon Rai da Haduwa a Aljannah. "

Post a Comment