--
Yanzu-Yanzu Lawan Ahmad Yasaki wani bayani Kan Soyayya da Fati Muhammad- Bbc Hausa News

Yanzu-Yanzu Lawan Ahmad Yasaki wani bayani Kan Soyayya da Fati Muhammad- Bbc Hausa News

>


Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya magantu a kan soyayyar da ya taba yi da tsohuwar jarumar masana'antar,


Fati Muhammad Lawan ya ce Allah bai yi zai auri Fati bane domin har maganar aure ta shiga tsakaninsu a wancan lokacin Sai dai kuma, ya ce tun bayan ita, bai sake kulla soyayya da wata 'yar fim 



Shahararren jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya bayyana cewa ya taba soyayya da tsohuwar jarumar masana’antar, Fati Muhammad a shekarun baya.


Lawan ya ce a wancan lokacin har magana ta yi karfi tsakaninsu, domin manya sun shiga lamarin ana ta maganar aure.


Lawan Ahmad ya ce ya taba soyayya da Fati Muhammed har maganar aure ya shiga tsakani amma abun bai yiwu ba Hoto:


Sai dai kuma jarumin ya ce ana tsaka da maganar auren ne sai maganar ta wargaje domin Allah bai yi za su zama mata da miji ba. Ya kuma ce tun bayan ita bai kara soyayya da wata yar fim ba.


Jarumin ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa a wata hira a shirin ‘Daga bakin mai ita’ na



ta tambaye shi ne kan ko ya taba soyayya da wata a masana’antar ta Kannywood, sai ya ce: “Mun taba soyayya da Fati Muhammad wacce har maganar aure ma ta dan shiga tsakaninmu da ita, toh amma da yake ka san komai nufi ne na Ubangiji, a wancan lokacin Allah bai yi ba. Shikenan ita ce kadai muka yi soyayya da ita, amma daga ita gaskiya ban kara soyayya da wata ‘yar fim ba.”


Cikakken bidiyon 👇

https://youtu.be/JbqsSSeDzZ8

0 Response to "Yanzu-Yanzu Lawan Ahmad Yasaki wani bayani Kan Soyayya da Fati Muhammad- Bbc Hausa News "

Post a Comment