Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun Kai hari a Karamar Hukumar Dandume jihar Katsina
Thursday 17 February 2022
Comment
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, suna cen suna harbin mutane a garin Abasawa da ke karamar hukumar Dandume jihar Katsina.
Lamarin na faruwa ne yanzu haka cikin daren nan, inda dayawan mutane suna guduwa domin ceton rayukansu.
Wani mazaunin garin ya bayyanawa jaridar arewa cewa yanzu haka sun kashe mutum 1, sun kuma raunata da dama daga cikinsu.
Zuwa yanzu dai ba a san adadin mutanen da aka harba ba, duk da dai wasu an dauke su zuwa babbar Asibiti don yi masu magani.
0 Response to "Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun Kai hari a Karamar Hukumar Dandume jihar Katsina"
Post a Comment