--
Kalli hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos Gwamnatin tarayya na Nemansu Ruwa A Jallo

Kalli hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos Gwamnatin tarayya na Nemansu Ruwa A Jallo

>


An kaddamar da yunkurin damko fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Jos, jihar Plateau Hukumar gidajen gyara hali 


NCoS ta yi kira ga yan Najeriya su taimaki hukuma wajen damkosu An kaddamar da bincike don sanin matsalar da aka samu suka gudu, 


Hukumar gidajen gyara hali a ranar Juma'a, 9 ga Yuli, ta saki hotunan fursunonin da suka gudu daga Kurkukun da ke Jos, birnin jihar Plateau. 


Hukumar ta bayyana hotunan a shafinta na Facebook mai taken: Fuskokin fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Jos. An shawarci yan Najeriya da ke da labari kan inda za'a gano wadannan mutane su tuntubi ofishin yan sanda mafi kusa. 


Yadda suka gudu Kontrolan yankin, Samuel Aguda, ya bayyana yadda suka gudu daga gidn yarin. Aguda ya ce sakacin jami'an dake tsare fursunonin ne ya haifar da hakan.


 Yace: "Lokacin da nazo wajen. Na lura cewa ko dai sun samu kofin makullin gidan yari ne ko kuma sakaci daga bangaren jami'ai." 


"Ta katanga suka arce." Ya kara da cewa mutum hudun na tsare ne gabanin gurfanar su a kotu kan laifin garkuwa da mutane da fashi da makami.


Makiyaya ne suka gudu Wata majiya ta bayyanawa manema labarai cewa wadannan fursunoni da ake zargin makiyaya ne sun gudu daga gidan yarin ne cikin daren Alhamis, 8 ga Yuli. The Nation ta kara da cewa makiyayan da suka gudu sun gurfana gaban kotun majistare dake karamar hukumar Barkin Ladi a shekarar 2020. 


Source: Legit 

0 Response to "Kalli hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos Gwamnatin tarayya na Nemansu Ruwa A Jallo"

Post a Comment