--
Da duminsa: Ba'a ga watan Zhul-Hajji a Saudiyya ba, ranar 20 ga Yuli Sallar Layya

Da duminsa: Ba'a ga watan Zhul-Hajji a Saudiyya ba, ranar 20 ga Yuli Sallar Layya

>


Rahoton dake shigo mana da duminsa daga kasar Saudiyya na nuna cewa ba'a ga jinjirin watan Zhul-Hijja 1442 ba a fadin kasar.


Haramain Sharifain da Haramain Live sun ruwaito cewa wannan ya biyo bayan fita neman jinjirin watan da masana suka yi da yammacin Juma'a.


Saboda haka, ranar Lahadi, 11 ga Yuli zai zama 1 ga watan Zhul Hijjah kuma ranar 20 Yuli zai zama ranar Babbar Sallah. Ranakun la'akari: 


Ranar 19 ga Yuli (9 ga Zhul Hijjah) - Ranar hawan Arafah ga mahajjata Ranar 20 ga Yuli (10 ga Zhul-Hujjah) - Ranar Sallah 0 Response to "Da duminsa: Ba'a ga watan Zhul-Hajji a Saudiyya ba, ranar 20 ga Yuli Sallar Layya"

Post a Comment